An haifi ‘yan uku masu dauke da COVID-19

Likitoci sun tabbatar da cewa wasu jarirai ‘yan uku da aka haifa na dauke da cutar COVID-19 bayan an yi musu gwajin cutar a kasar Mexico. Jami’an kiwon lafiya a kasar sun tabbabtar cewa babu wani mai cutar da ya taba jariran ko ya yi wata mu’amala da su in banda mahaifiyarsu. Hakan ya sa masana […]

An haifi ‘yan uku masu dauke da COVID-19

Likitoci sun tabbatar da cewa wasu jarirai ‘yan uku da aka haifa na dauke da cutar COVID-19 bayan an yi musu gwajin cutar a kasar Mexico.

Jami’an kiwon lafiya a kasar sun tabbabtar cewa babu wani mai cutar da ya taba jariran ko ya yi wata mu’amala da su in banda mahaifiyarsu.

Hakan ya sa masana a harkar lafiya fara nazari ko uwa na iya gadar wa jaririn da take dauke da shi a mahaifar cutar ta COVID-19.

Ma’aikatan lafiya su ce an haifi jariran ne a ranar 8 ga watan Mayu kuma mahaifiyarsu da ubansu na dauke da cutar, sai dai alamun cutar ba su bayyana a jikinsu ba.

Sakatariyar Kiwon Lafiya ta Arewacin kasar Mexico, Monica Rangel ta shaida wa kafar yada labarai ta New York Times cewa jariran ba sa cikin hadari, sai dai ana bincike domin a gano ko sun harbu da cutar ne kafin a haife su ko kuma bayan an haifesu.

Shin uwa na iya ba wa dan da ke cikinta COVID-19?

Wannan lamari ya sanya masana kiwon lafiya fara nazarin ko uwa za ta iya ba wa dan da ke cikin mahaifarta cutar coronavirus.

New York Times ta ce idan bincike ya nuna haka ne, ‘yan ukun za su kasance cikin yara kalilan da aka haifa da cutar a duniya.

Sai dai zuwa yanzu babu wadatattun bincike da aka yi akan wannan mas’ala ta ko uwa kan iya shafa wa dan da ke mahaifarta cutar.

Shin uwa mai COVID-19 na iya taba danta?

Jawaban da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi a kan wannan maudu’i shi ne uwa ta ba wa dan da ta haifa kulawar da ta kamata, ta ja shi a jika, ta shayar da shi, ta kuma kwana a daki daya da shi.

Sai dai WHO ta ce uwar dan ta tabbatar ta wanke hannunta da kyau kafin ta dauke shi da kuma bayan hakan.

Sai dai kuma idan uwar na fama da matsalar numfashi ne, to nan kuma sai a kiyaye kusancinta da dan.

Rahotanni sun nuna cewa a fadin duniya yara kalilan ne suka kamu da COVID-19 kuma mafi akasari  yara kanana ba su cika shiga hadari a sakamakon cutar ba.