An haifi yarinya da hancin giwa a Indiya

A ranar Alhamis din makon jiya ne wata mata a wani kauye a Jihar Uttar Pradesh da ke arewacin kasar Indiya ta haifi wata yarinya mai hancin giwa. Yarinyar wacce har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a rada mata suna ba tukuna. Har ila yau, tun bayan haihuwarta ne dubban mutane suke tururuwa zuwa […]

An haifi yarinya da hancin giwa a Indiya
An haifi yarinya da hancin giwa a Indiya

A ranar Alhamis din makon jiya ne wata mata a wani kauye a Jihar Uttar Pradesh da ke arewacin kasar Indiya ta haifi wata yarinya mai hancin giwa.

Yarinyar wacce har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a rada mata suna ba tukuna. Har ila yau, tun bayan haihuwarta ne dubban mutane suke tururuwa zuwa kauyen domin yin tozali da ita. Mutanen suna haka ne saboda amannar da suka yi cewa wani abin bautarsu ne mai suna Ganesha, wanda ya bayyana a matsayin jinjirar.
Innar jinjirar ta bayyana wa jaridar Daily Mirror cewa gungun masu bauta ne suke ziyartarsu domin bai wa jinjirar kyautar neman tabarraki. Ta ce: “Mai jegon mai suna Banna Debi ta haife ta ne da misalin karfe bakwai na safe kuma fuskarta ta yi kama sosai da abin bautanmu wato Lord Ganesha. Wannan ya sa duk wanda ya samu wannan labarin yake zuwa nan domin yin ido hudu da ita da kuma ba ta kowace irin kyauta,” inji ta.
Yarinyar wacce ita ce ta hudu a wajen iyayenta, tana da wata lalura ne a fuskarta, inda a tsakakanin idanuwanta biyu take da wani abu mai kama da hancin giwa wanda kuma ya raba hancin nata gida biyu tun lokacin da take ciki. A halin yanzu dai likitoci suna nazarin lalurar saboda gano hanyoyin da za su yi mata aiki domin daidaita ta kamar sauran jama’a. Kuma sun ce ta iya yiwuwa lalurar ta faru ne saboda rashin isasshen abinci daga bangaren mai jegon lokacin da take goyon cikin da kuma gurbacewar muhalli.
Mahaifin jinjirar mai suna, Mista Sarbesh ya ce yana samun rupee 250 a rana (wato kimanin naira 750) saboda haka yake fatan haihuwar yarinyar zai kara bude wa iyalinsa hanyoyin arziki.