An haifi yarinya da zuciyarta akan kirji

A ranar Larabar makon jiya ne wata mata a garin Dindori da ke kasar Indiya ta haifi wata jinjira mai zuciya a waje, a samar kirjinta.  Mai jegon mai suna Sushma, ’yar kimanin shekara 22 ta haife yarinyar ne da kimanin karfe 12 na rana, kamar yadda babban likitan asibitin Dokta G K Samad ya […]

An haifi yarinya da zuciyarta akan kirji
An haifi yarinya da zuciyarta akan kirji

A ranar Larabar makon jiya ne wata mata a garin Dindori da ke kasar Indiya ta haifi wata jinjira mai zuciya a waje, a samar kirjinta. 

Mai jegon mai suna Sushma, ’yar kimanin shekara 22 ta haife yarinyar ne da kimanin karfe 12 na rana, kamar yadda babban likitan asibitin Dokta G K Samad ya bayyana wa jaridar Mirror da ke Birtaniya. Likitoci sun ce irin lalurar ba a cika samunta ba sosai, inda akan same ta a cikin jirajirai takwas bayan haihuwar yara akalla miliyan daya. Kuma tara cikin 10 na wadanda ake haihuwa da lalurar suna zuwa ne ba rai, ko kuma su rasu kwanaki kadan bayan haihuwarsu.
Maihaifin jinjirar mai suna, Basant Padmaker ya ce: “Ubangiji ya albarkaci mu da wannan haihuwa, amma ban san ko zan kira abin alheri ba, ko kuma akasin hakan. Saboda ba ni da karfi. Da kyar muke samun cin abinci sau biyu a rana. Amma zan yi dukkan mai yiwuwa domin ceto wannan yarinyar.”
Za dai a yi wa jinjirar aiki ne a wani asibitin kwararru da ke kasar, kuma jagoran likitocin da za su yi aikin, Dokta bikesh Agarwal ya ce suna tabbacin cewa za a samu nasara bayan kammala aikin.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume