An haifi yaro da lamba “12” a goshinsa

An haifi wani yaro da lamba “12” a goshinsa a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu. Masana dai sun bayyana cewa lambar da aka haifi yaran da ita a kan goshinsa ba 13 ba ce wadda ke inkari da rashin sa’a. Kuma likitoci samun lamba 12 a bisa goshin yaran a zagaye abin mamaki […]

An haifi yaro da lamba “12” a goshinsa
An haifi yaro da lamba “12” a goshinsa

An haifi wani yaro da lamba “12” a goshinsa a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.

Masana dai sun bayyana cewa lambar da aka haifi yaran da ita a kan goshinsa ba 13 ba ce wadda ke inkari da rashin sa’a. Kuma likitoci samun lamba 12 a bisa goshin yaran a zagaye abin mamaki yadda lambar ta bayyana baro-baro.
Yaron mai suna Hanru ban Niekekerk , an haife shi ne ranar 11 ga watan Nuwamban bara domin haka masana ke cewa lambar ranar ba ta yi daidai da ranar haihuwar sa ba, kuma iyalansu ba su danganta abin da wani abu da ke da alaka da rayuwarsu ba.
Kakan jinjirin Catherine Jooste ta ce: “Wata diyata ce ta fara ganin abin, sai ta ce akwai numba 1 da 2 a goshinsa,” inji ta kamar yadda ta bayyana wa jaridar Northcliff Melbille Times.
Dattijon mai shekara 70 ya kara da cewa ba mu da wata damu da faruwar wannan al’amari, saboda likitoci sun ce yau da gobe lambar za ta bace da kanta.
Koma me ye dalilin faruwar hakan yaron Hanru zai samu abin magna a saukake a lokacin da ya girma. Kamar yadda hukumar lafiya ta ce tambarin da ake haihuwa mutum da shi yana faruwa ne daga cikin manyan suffofi biyu hanyar jini ko sanadarin launin fatar dan Adam. Kuma tambarin da ake haihuwar mutum da shi mafi yawa yana faruwa ne ko saboda wuya, dalilin rashin aikin hanyar jini yadda ya kamata a cikin ko karkashin fata, wanda zai iya gogewa bayan wasu watanni kalilan.