‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyu a Kaduna
Wasu ‘yan bindiga da ba a tantance su ba, sun budewa wasu ‘yan sanda wuta a safiyar yau Laraba. ’yan sandan dai na gadin kamfanin giya ne na ‘International Beer and Beverage Industries, IBBI’, dake unguwar Nasarawa, a hanyar Nnamdi Azikiwe bypass, dake Kaduna. Rahotan na bayyana cewa, ‘yan bindigan sun bude wa ‘yan sandan […]
Wasu ‘yan bindiga da ba a tantance su ba, sun budewa wasu ‘yan sanda wuta a safiyar yau Laraba. ’yan sandan dai na gadin kamfanin giya ne na ‘International Beer and Beverage Industries, IBBI’, dake unguwar Nasarawa, a hanyar Nnamdi Azikiwe bypass, dake Kaduna.
Rahotan na bayyana cewa, ‘yan bindigan sun bude wa ‘yan sandan wuta ne lokacin sallar asuba, yayin da ‘yan bindigar suka yi shiga kamar zasu je yin sallar asuba, amma daga bisani suka budewa jami’an tsaron wuta nan ta ke suka kashe biyu.