An hallaka Bahaushe da farkarsa a Layin Jahannama a Ibadan
Matar mai zaman kanta mai suna Maman Dadi ita ma ta rasa ranta bayan daba mata wuka a sassan jikinta.
An yi wa wani matashi mai suna Bashar kisan gilla ta hanyar yankan rago a cikin dakin wata mata mai zaman kanta mai suna Maman Dadi wacce ita ma ta rasa ranta bayan daba mata wuka a sassan jikinta.
Lamarin ya auku ne cikin dare a ranar Juma’a da ta gabata a wani sashe da ake kira Layin Jahannama da ke garejin manyan motoci na kauyen Akinyele a kusa da birnin Ibadan, hedkwatar Jihar Oyo.
A lokacin da Aminiya ta ziyarci wurin washegari Asabar ta tarar da daruruwan dakunan katako da leda inda mata masu zaman kansu suke zaune a ciki duka an kulle su.
Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta ce “Babban Jami’in ’Yan sandan yankin Moniya ya ziyarci wannan wuri jim kadan bayan aukuwar lamarin inda ya umarci jami’ansa su kwashe gawarwakin mutanen zuwa asibiti tare da kama shugabannin wurin.
“Ganin an kama shugabannin ne ya sa sauran mata masu zaman kansu suka fara kulle dakunansu suna kaurace wa wurin saboda tsoron abin da ka iya biyo baya.
“Wadanda ’yan sandan suka kama a cikin daren sun hada da Sani Dan Karuwa da Sule Meri da Alhaji Umar da magajiyar wurin, Iya Remi wacce ta kai kanta ga ’yan sanda da kuma mataimakiyarta Hadiza.
“An tasa keyarsu zuwa ofishin ’yan sanda na Moniya domin yi musu tambayoyi.
“Wata majiyar ’yan sanda ta ce an kama su ne don yi musu tambayoyin da zai kai ga bankado dalilin aukuwar lamarin da kama ainihin wadanda suka yi kisan gillar.
“Ba mu kama su kan zargin aikata wani laifi ba tukunna.”
Har ila yau wata majiya ta daban ta ce, “Mutanen da suka fara shiga cikin dakin matar kafin isowar ’yan sanda, sun tarar da gawar matashin da aka yi wa yankan rago kwance cikin jini yana malala a yayin da ita mai dakin take numfashi sama-sama kafin ta karasa a hanyar zuwa asibiti a dalilin munanan raunuka da ta samu a sassan jikinta.
“Duk da yake ba mu tabbatar ba amma hasashen wasu daga cikin mu ya karkata ne ga cewa watakila daya daga cikin maneman matar ce ya tarar da bakon mutum a cikin dakin, inda ya yanke wa kansa hukunci ta hanyar yi musu kisan gilla saboda kishi.”
Binciken da Aminiya ta gudanar ta gano cewa matashin da aka yi wa yankan rago dan asalin Jihar Kano ne da yake yin sana’ar kanikancin mota a cikin garejin manyan motoci na Akinyele.
Kuma an tabbatar da cewa danginsa sun kammala shirin kai kudin aurensa nan da mako biyu masu zuwa sai ga labarin mutuwarsa a irin wannan yanayi da ba su zata ba, saboda shaidar da aka yi masa na kamun kai da mayar da hankalinsa a kan sana’arsa.
Matar kuma an gano ta fito ne daga Zariya a Jihar Kaduna bayan aurenta ya mutu inda ta yanke shawarar zaman karuwanci a wannan wuri.
Binciken ya gano cewa mafi yawancin matan da suke karuwanci a ‘Layin Jahannama’ kananan ’yan mata ne da suka fito daga garuruwan Arewa.
Daya daga cikin shugabannin garejin na Akinyele da aka sakaya sunansa ya ce “Irin wannan lamari bai taba aukuwa cikin shekara 17 da muka yi da tarewa a wannan gareji ba.
“Gaskiya ce ana samun sabani da rashin jituwa a tsakanin mazauna wannan wuri, inda shugabannin garejin suke sasantawa da hukunta mai laifi, idan ya gagare su kuma sai su mika lamarin ga ’yan sanda.
“Amma ba a taba samun irin wannan ba a tsawon wannan lokaci.”
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo kan wannan lamari sai dai ba ta yi nasara ba.