An hallaka mutane da yawa a sabon fadan Nasarawa
Mutum 14 da suka fito daga kabilar Tibi ne ake zaton sun rasa rayukansu, yayin da aka sace shanu da dama a wani sabon fada da ya barke a tsakanin Fulani makiyaya da Tibi manoma da suke kauyukan kananan hukumomin Keana da Obi da Awe da ke Jihar Nasarawa. Aminiya ta samu bayanin cewa ana […]

Mutum 14 da suka fito daga kabilar Tibi ne ake zaton sun rasa rayukansu, yayin da aka sace shanu da dama a wani sabon fada da ya barke a tsakanin Fulani makiyaya da Tibi manoma da suke kauyukan kananan hukumomin Keana da Obi da Awe da ke Jihar Nasarawa.
Aminiya ta samu bayanin cewa ana zaman dar-dar a yankunan tun lokacin da aka kashe Fulani matafiya a wani yankin na iyakar Jihar Benuwai, kuma lamarin ya kazance ne a ranar Litinin da ta gabata inda aka samu labarin hallaka mutum 14 a kauyukan yankin Obi, sakamakon zargin kashe wani makiyayi da sace masa shanu a ranar Lahadin da ta gabata da ake zargin manoma ’yan kabilar Tibi da aikatawa.
Wakilinmu ya samu labarain cewa sama da ’yan kabilar Tibi 1,400 ne suka gudu daga gidajensu suka koma zaman hijira a Lafiya fadar jihar, inda wadansu suke zaune a sansanonin ’yan gudun hijira daban-daban da ke jihar.
Wakilinmu ya ziyarci Asibitin kwararru na dalhatu Araf da ke Lafiya inda ya iske mutum 8 daga cikin mutanen da lamarin ya shafa suna jinya, kuma ya ga gawarwakin mutum 5 a dakin ajiyar gawarwaki na asibitin.
Shugaban kungiyar Matasan kabilr Tibi a Jihar Nasarawa, Kwamared Peter Ahemba ya ce ’yan bindigar sun kai munanan hare-hare a kusan dukan kauyukan Tibi da ke yammacin jihar. Ya ce “A yanzu da nake yi muku bayyani mun gano gawarwakin mutanenmu 7 wadanda Fulani ’yan bindiga suka kashe wadanda jami’an tsaro suka kai su garin Keana daga bisani aka kai su Asibitin kwararru na dalhatu da ke Lafiya.” Kwamared Ahemba ya ce Fulani ’yan bindigar suna shiga kauyukan Tibi ne a cikin manyan motoci da suka hada da tirela da tifa da sauransu. Ya nuna takaicinsa game da aukuwar lamarin inda ya yi kira ga gwamnatin Jihar Nasarawa ta dauki mataki cikin gaggawa don kawo karshen lamarin kuma ya bukaci Gwamnatin Tarayya da kasashen duniya su sa baki cikin lamarin domin kawo karshen kisan a jihar da kasa baki daya.
Shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta Jihar Nasarawa, Alhaji Muhammad Hussaini ya ce mayakan Tibi a ranar Litinin sun mamayi wasu sassa na kananan hukumomin Keana da Obi dauke da miyagun makamai suna kashe duk Bafulatani makiyayi da suka ci karo da shi a nahyarus ta zuwa lalata gidajensu.
Hussaini ya yi zargin cewa mayakan Tibi sun hada baki da danginsu daga Jihar Benuwai inda suka shirya kai miyagun hare-haren da ya hallaka mutane da dama. Ya ce: “A yanzu da muke magana da kai an kwashi gawarwaki 7 zuwa Ofishin Shiyya na ’Yan sandan Keana, yayin da dama suke yaryashe a daji.”
Kakakin ’Yan sandan Jihar ASP Idirisu Kenedy da wakilinmu ya tuntube shi ya tabbatar da aukuwar rikicin, inda ya ce tuni suka turo jami’ansu inda lamarin ya auku domin dawo da doka da oda, amma ba a sanar da shi adadin mutanen da suka rasu ba.