An hallaka mutum 37 a Afghanistan

Hukumomin kasar Afghanistan sun ce mutum 37 cikinsu har da mata da kananan yara ne suka rasu a wani hari da ake zargin kungiyar Taliban ta kai a filin jirgin sama da ke birnin Kandahar.Rahotanni sun ce har zuwa lokacin hada wannan rahoto  akwai daya daga cikin mayakan da ake ta fafatawa da shi a […]

An hallaka mutum 37 a Afghanistan
An hallaka mutum 37 a Afghanistan

Hukumomin kasar Afghanistan sun ce mutum 37 cikinsu har da mata da kananan yara ne suka rasu a wani hari da ake zargin kungiyar Taliban ta kai a filin jirgin sama da ke birnin Kandahar.
Rahotanni sun ce har zuwa lokacin hada wannan rahoto  akwai daya daga cikin mayakan da ake ta fafatawa da shi a cikin filin saukar jiragen saman, inda sansanin kungiyar tsaro ta NATO da hedikwatar dakarun sojin Afghanistan suke.
Jami’ai sun tabbatar da mutuwar mayakan kungiyar su tara.
An kai harin ne da yammacin ranar Talatar da ta gabata, lokacin da wasu mayakan na Taliban dauke da manyan makamai suka shiga cikin sansanin sojojin.
Wasu cikin mayakan Taliban din sun kwace iko da wata makaranta da ke kusa da sansanin, inda suka mayar da ita wurin bude-wuta, domin agaza wa sauran mayakan nasu.
Kodayke, wata sanarwa da ta fito daga kungiyar Taliban ta ce sun kashe sojoji akalla 80. Amma ba za a iya tabbatar da hakan ba tukuna.