An hallaka ’yan sanda uku a Fatakwal
Wasu da ake kyautata zaton ’yan daba ne sun kashe ’yan sanda uku da ke aiki da Rundunar ’Yan sandan Jihar Ribas a garin Fatakwal. Jami’an ’yan sandan, kamar yadda Aminiya ta samu labari, an samu tabbacin cewa gungun wasu ’yan ta’adda ne da wani dan siyasa yake zargi na yunkurin hallaka shi ya gayyato […]
Wasu da ake kyautata zaton ’yan daba ne sun kashe ’yan sanda uku da ke aiki da Rundunar ’Yan sandan Jihar Ribas a garin Fatakwal.
Jami’an ’yan sandan, kamar yadda Aminiya ta samu labari, an samu tabbacin cewa gungun wasu ’yan ta’adda ne da wani dan siyasa yake zargi na yunkurin hallaka shi ya gayyato su da nufin su ba shi kariya, su kore su. Musayar wuta tsakanin ’yan bindigar da ’yan sanda ce ta yi sanadiyyar ajalinsu.
dan siyasar Jerry Needam wanda mai ba Shugaban Jam’iyyar PDP shawara ta musamman ne, aka kai wa harin, shi kuma ya kirawo ’yan sandan, domin su kawo masa taimakon gaggawa. Kuma lokacin da suka isa ne aka samu musayar wuta a tsakaninsu da maharan inda suka hadu da ajalinsu.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan sandan Jihar Ribas, Muhammad Kaliya bai bayyana sunayen jami’an da suka rasu ba amma ya tabbatar da aukuwar lamarin.