An hana amfani da Facebook da WhatsApp saboda daure Ousmane Sonko a Senegal
An same Sanko da laifin nuna rashin da’a, amma an wanke shi daga zargin aikata fyade.
Hukumomi a Senegal sun toshe hanyoyin shiga shafukan sada zumunta da muhawara da suka hada da Facebook da WhatsApp sakamakon kazamin rikicin da ake fuskanta a kasar.
Bayanai sun ce rikicin dai ya biyo bayan hukuncin daurin shekara biyu da kotu ta yanke wa jagoran ’yan hamayya na kasar, Ousmane Sonko.
- Tallafin Man Fetur: NLC za ta tsunduma yajin aiki ranar Laraba
- An ceto direbobin da ISWAP ta yi garkuwa da su a Borno
Daman gwamnatin ta ce za ta dau duk wani mataki da ya dace domin kare rayuwar al’umma da dukiyoyi bayan mutuwar mutane sakamakon rikicin.
Akalla mutum tara ne suka mutu a rikici tsakanin ’yan sanda da masu zanga-zanga, bayan yanke wa Ousmane Sonko hukuncin a jiya Alhamis, inda aka rika kona motoci a Dakar.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Antoine Diome a wani taron ’yan jarida a cikin dare, ya ce an toshe kafofin ne, yana mai nuna takaicin abubuwan da suka faru.
Rikicin ya fi baci a yankin Ziguinchor – (Zi-gan-shiyo)- da ke Kudancin kasar, inda Mista Sonko ke rike da mukamin magajin gari.
Hukukuncin kotun da aka yanke a bayan idonsa na iya hana shi tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa.
An same shi da laifin nuna rashin da’a, amma an wanke shi daga zargin aikata fyade.
Hukuncin dai na iya shafar yunkurin Sonko na tsayawa takarar shugabancin kasar, yayin da yake kokarin fafatawa da Shugaba Macky Sall.
Wannan shari’a dai ta haifar da rarrabuwar kawuna a Senegal, abin da ya haifar da rikici mafi muni a tarihin kasar.