An hana amfani da lasifika wajen kiran sallah a Ruwanda
Gwamnatin Ruwanda ta haramta yin amfani da lasifika wajen kiran sallah a duk masallatan da ke babban birnin kasar. An dauki wannan matakin ne saboda koke-koken da mutanen suke yi na cewa ana damunsu, musamman wadanda suke makwabtaka da masallatai. Amm wata kungiyar musulmi a Rwanda ta soki matakin, inda suka ce kamata ya yi […]

Amm wata kungiyar musulmi a Rwanda ta soki matakin, inda suka ce kamata ya yi a bukaci da su rage karar lasifikar.
A kwanan baya ma gwamnatin Rwanda ta rufe coci sama da 700 saboda dalilai na tsaro da kiwon lafiya.
Mafi yawan mutanen Ruwanda kirista ne, kashi biyar cikin dari ne kawai mabiya addinin musulunci.