An hana azumi a wani yankin kasar China

Mahukunta a kasar China sun hana ma’aikatan gwamnati da dalibai da kuma malamai daukar azumin watan Ramadan a yankin dinjiang, inda kuma aka umarci gidajen cin aminci su kasance a bude, kamar yadda shafin intanet din gwamnatin kasar ya bayyana. A galibin kasashen duniya dai, an fara azumin ne jiya Alhamis. Kodayake, ba wannan ba […]

An hana azumi a wani yankin kasar China
An hana azumi a wani yankin kasar China

Mahukunta a kasar China sun hana ma’aikatan gwamnati da dalibai da kuma malamai daukar azumin watan Ramadan a yankin dinjiang, inda kuma aka umarci gidajen cin aminci su kasance a bude, kamar yadda shafin intanet din gwamnatin kasar ya bayyana.

A galibin kasashen duniya dai, an fara azumin ne jiya Alhamis. Kodayake, ba wannan ba ne karon farko da jam’iyyar ’yan gurguzu da take mulkin kasar take haramta azumin a yankin, wanda yake yawan mabiya addinin Musulunci, ’yan kabilar Uighur marasa rinjaye.
Wata kungiya da take fafutukar kwato ’yancin Musulmin a yankin ta ce wannan wani abu da zai iya rura wuta da zaman tankiyar da ya dade a yankin. Har ila yau, a bara, yara ’yan amkaranta suna cikin wadanda aka haramta wa daukar azumin.
Ma’aikatar Ilimin kasar a wannan watan ta umarce makarantu da su tabbatar da sun “hana duk wani dalibi Musulmi daukar da shiga masallaci da sauransu.”