An hana mu kai dauki Gamboru – Soja

Wani sojan da ke aikin dawo da zaman lafiya a Jihar Borno ya yi zargin cewa a gaban idonsu ’yan kungiyar Boko Haram suka kai hari a garin Gamboru-Ngala a makon jiya inda suka kashe mutum 300, amma kwamandansu ya ki ba su umarnin su kai dauki ga mutanen da harin ya rutsa da su.Sojan […]

An hana mu kai dauki Gamboru – Soja
An hana mu kai dauki Gamboru – Soja

 Janar Kenneth Tobiah Minimah Hafsan Hafsoshin Sojan NajeriyaWani sojan da ke aikin dawo da zaman lafiya a Jihar Borno ya yi zargin cewa a gaban idonsu ’yan kungiyar Boko Haram suka kai hari a garin Gamboru-Ngala a makon jiya inda suka kashe mutum 300, amma kwamandansu ya ki ba su umarnin su kai dauki ga mutanen da harin ya rutsa da su.
Sojan wanda ya shaida wa gidan rediyo BBC Landan haka kuma aka boye sunansa, ya ce ko baya ga su sojan kasa har da jirgin saman yaki ya zo yana shawagi a sararin samaniyar garin a lokacin da harin ke gudana amma ba a ba shi umarnin kai dauki ba.
Da ma wadanda suka tsira daga harin na Gamborun-Ngala sun nemi a janye sojojin daga garin saboda a cewarsu ba su yi musu wata rana ba lokacin da harin ke gudana.
Sojan ya kara da cewa suna zargin wannan hari da aka kai na hadin baki ne, saboda rashin hana su aiwatar da aikinsu.
Haka kuma ’yan banga da ake kira ’yan kato da gora da ke aiki a cikin Gamboru-Ngala sun ce maharan ba su je da makamai masu yawa ba.
Sojan ya ce idan har manyansu ba su cire hannunsu a harkar Boko Haram ba, to kuwa ba za a yi nasara ba a yakin da ake yi da kungiyar.