An hana Musulmi yin zabe a kasar Bama
A jibi Lahadi ne za a gudanar da babban zabe a kasar Bama, sai dai miliyoyin Musulmin da ke kasar ba a ba su damar tsayawa takara ba, kuma ba za su kada kuri’arsu ba a zaben.Yawan Musulmin kasar ya kai kashi biyar cikin 100 na al’ummar kasar miliyan 51. Babu Musulmi ko da guda […]
A jibi Lahadi ne za a gudanar da babban zabe a kasar Bama, sai dai miliyoyin Musulmin da ke kasar ba a ba su damar tsayawa takara ba, kuma ba za su kada kuri’arsu ba a zaben.
Yawan Musulmin kasar ya kai kashi biyar cikin 100 na al’ummar kasar miliyan 51. Babu Musulmi ko da guda da yake takara a duka jam’iyyun siyasar kasar. Jam’iyyar adawa ta National League for Democracy (NLD), wadda mai fafutukar dimukradiyya, Aung San Suu Kyi, ke jagoranta, ta ce ta hana ’yan siyasa Musulmi tsayawa takara ne a karkashinta saboda matsin lambar da take fuskanta daga kungiyoyin addinin Buddha da ke kasar, wadda wasu suke kira Myanmar.
Hakazalika, fiye da Mulsulmi miliyan guda ’yan kabilar Rohingya da wasu Musulmi daga kananan kabilu da ke yankin Kudancin kasar ba za su samu damar kada kuri’arsu ba a zaben. Wannan ba ya rasa nasaba da yadda hukumomin kasar suka hana Musulmi mallakar takardun shaidar zama ’yan kasar saboda ana musu kallon su baki ne, ba ’yan kasa ba.
Kodayake, akwai kasashen duniya da dama ciki har da Birtaniya da Amurka da suke bai wa baki damar kada kuri’a a lokutan zabe.