An hana ’yan jarida daukar zaman Kwamitin Amintattun PDP da Wike
Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP ya kori ’yan jarida daga dakin taron zaman da zai yi da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike.
Kwamitin Amintattun Jam’iyyar PDP ya kori ’yan jarida daga dakin taron shawo kan Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike.
Shugaban Kwamitin Amintattun, Sanata Adolphus Wabara ne ya bukaci ’yan jarida su fice daga dakin taron, bai ji dadin ganin su ba, duk da cewa Wike mai masaukin baki ya gayyato su.
A ranar Talata kwamitin yake zama da Wike a ofishinsa da ke Fatakwal, kan sa-toka-sa-katsi da ke tsakanin gwamnan da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar da kuma Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Iyorchia Ayu.
Gabanin zaman, Gwamna Wike ya gayyaci ’yan jarida da ke aiki a Gidan Gwamnatin Jihar Ribas domin daukar rahoton abin da zai wakana a zaman.
Sai dai bayan zuwan mambobin Kwamitin Amintattun, Sanata Adolphus Wabara ya bukaci su bar wajen kafin a fara tattaunawar.
Wakilinmu ya gano bayan kammala taken Najeriya a dakin taron ne Wabara ya bukaci a sallami daukacin ’yan jaridar.
A wani bidiyo da aka fitar, an ga Wike na tambayar Wabara ko yana bukatar ’yan jarida su dauki rahoton zaman.
An kuma ji gwamnan na cewa yana so ’yan jarida su halarci taron domin su samu damar bayar da rahoton hakikanin abin da ya faru.
Kafin nan, Wike ya bayyana rashin jin dadi bisa yadda ya ce ’yan jarida suka gurbata rahoton zaman da aka yi domin dinke barakar cikin gidan jam’iyyar ta PDP.