An hana ’yan jarida daukar hoto a kotun da za a yanke hukuncin zaben Gwamnan Kano

Jami’an ’yan sanda sun hana wasu ’yan jarida shiga kotun da za ta yanke hukunci kan zaben Gwamnan Jihar Kano.

An hana ’yan jarida daukar hoto a kotun da za a yanke hukuncin zaben Gwamnan Kano

Jami’an ’yan sanda sun hana ’yan jarida daukar hoto ko shiga da waya cikin kotun da za ta yanke hukunci kan zaben Gwamnan Jihar Kano.

Tun da sanyin safiya ne dai dandazon ’yan jaridar suka yi wa hanyar kotun da ke kan titin Miller Road a unguwar Bompai da ke Kano tsinke, amma aka hana su shiga.

’Yan sanda dai sun ce ’yan jarida 10 kawai aka kyale su bari su shiga kotun, daga bisani kuma aka kara adadin zuwa 15.

Sai dai galibin ’yan jaridar da suka rage sun yi ta gararamba a wajen, yayin da na cikin kuma suke dakon shiga ciki, kafin daga bisani su shiga.

Ko gabanin nan sai da aka ba hammata iska tsakanin wasu jami’an ’yan sandan da wasu ’yan jarida saboda daukar hoto.

A sakamakon haka, da ƙyar aka ƙwaci wakilin Sashen Hausa na BBC daga hannun ’yan sandan, sannan suka fasa wayar wakilin Daily Trust/Aminiya.

Matakan tsaro

An dai jibge jami’an tsaro daban-daban a dukkan hanyoyin da ke isa ga kotun da ma dukkan wasu muhimman wurare da ke Kano.

’Yan sandan dai sun ce gaba daya mutum 50 aka amince su shiga cikin kotun, tun daga ’yan siyasa, lauyoyi, ’yan jarida da jami’an tsaro.

Kawo yanzu dai kotun ba ta riga ta fara zama ba, amma kowanne lokaci daga yanzu za a iya shiga domin yanke hukuncin.

Idan za a iya tunawa, jam’iyyar APC ce dai ta kai kara kotun tana kalubalantar nasarar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu a zaben Gwamnan jihar na watan Maris.

Babban Limamin Minna Sheikh Isa Fari ya rasu

Saudiyya ta ɗauki malamai dubu 9 domin koyar da kaɗe-kaɗe a makarantu

‘Yar China na fuskantar saki bayan ta haifi jariri baƙar fata

A ƙofar banɗakin Gidan Yarin Kuje nake kwana — Ɗan zanga-zanga