An hana yara zuwa wuraren ibada – Sanwo-Olu
Ba za a bude masallatai ba sai nan da makonni biyu a jihar Legas, a cewar Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu. Gwamnan ya ce za a bude masallatai a jihar ranar 19 ga watan Yuni, su kuma coci-coci za a bude su ranar 21 ga wata. Ya kara da cewa ba a yarda ba yara ‘yan […]
Ba za a bude masallatai ba sai nan da makonni biyu a jihar Legas, a cewar Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu.
Gwamnan ya ce za a bude masallatai a jihar ranar 19 ga watan Yuni, su kuma coci-coci za a bude su ranar 21 ga wata.
Ya kara da cewa ba a yarda ba yara ‘yan kasa da shekara 15 su halarci tarukan ibada a ranakun Juma’a da Lahadi a jihar.
Babajide Sanwo-Olu ya sanar da haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar da ke Marina a ranar Alhamis.
Gwamnatin jihar ta sanar da haka ne yayin da take kokarin daukar matakan da suka dace domin takaita yaduwar cutar coronavirus.
Har yanzu jihar ce kan gaba wurin yawan masu cutar coronavirus a Najeriya kuma a jihar aka fara samu bullar cutar a kasar.