An hango su Ganduje suna gyangyaɗi a kotun sauraron karrakin zaben Shugaban Kasa

Sun yi gyangyadin ne yayin zaman kotun na ranar Laraba

An hango su Ganduje suna gyangyaɗi a kotun sauraron karrakin zaben Shugaban Kasa

Masu amfani da kafafen sada zumunta sun fara tsokaci kan hotunan wasu fitattun mutane sun gyagyaɗi a kotun sauraron kararrakin zabe da ke Abuja ranar Laraba.

Daga cikin mutanen har da Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnan Jihar Bauchi, Baka Mohammed da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo da lauyoyi da wasu ’yan jarida.

Ana dai yanke hukuncin ne a kan wasu krarraki guda uku da ke kalubalantar sakamakon zaben Shugaban Kasa na ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata.

Ga wasu daga cikin hotunan:

Hajjin 2023: An dawo wa mahajjata 3,000 kuɗaɗensu a Kaduna

’Yan sanda sun ceto mutum 23 da aka sace a Kaduna

Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Man City da ci 5

Fasinjoji 30 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Ondo