An haramta acaba da daddare a Jihar Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta hana ’yan acaba da masu babura na kashin kansu yawon dare daga karfe 10:00 na dare zuwa karfe 6:00 na safe. Gwamnatin ta kara da cewa, hukumomin tsaro na nan domin sa ido ga duk wanda ya karya wannan doka. Haka nan kuma jami’an tsaro ba za su lamunce wa kowa […]

An haramta acaba da daddare a Jihar Kebbi
An haramta acaba da daddare a Jihar Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta hana ’yan acaba da masu babura na kashin kansu yawon dare daga karfe 10:00 na dare zuwa karfe 6:00 na safe. Gwamnatin ta kara da cewa, hukumomin tsaro na nan domin sa ido ga duk wanda ya karya wannan doka. Haka nan kuma jami’an tsaro ba za su lamunce wa kowa ba muddin ya saba dokar. Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Nura Usman Kangiwa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar bayan ganawa da shugabannin hukumomin tsaro a ofishinsa da ke Birnin Kebbi.
Ya ce jami’an tsaro za su ci gaba da sintiri babudare babu rana a ko’ina cikin jihar, sintirin wanda tuni rundunar ’yan sandan jihar take domin kare lafiyar jama’a da rayukansu. Ita dai wannan doka ta shafi kananan hukumomi 21 da ke Jihar Kebbi da kuma garuruwan Bena da Danko da Ka’oje. Sanarwa ta nuna cewa wannan doka za ta taimaka wajen kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu kamar yadda dokar kasa ta tanada. HaKa kuma sanarwar ta yi kira ga jami’a su ba gwamnati hadin kai domin ganin jami’an tsaro sun gudanar da aikinsu bisa nasara. Dokar ta yi sassauci ga ma’aikatan asibiti da sauran masu gudanar da ayyuka na musamman kamar ma’aikatan kamfanin lanatarki na kasa da ma’aikatan hukumar ruwa da na hukumar kashe gobara da makamantansu.