An haramta amfani da labule a Keke-NAPEP
Shugaban Hadin Gwiwar Jami’an Tsaro na Jihar Kaduna (Operation Yaki) Yakubu Yusuf Soja ya gargadi masu saka labule a Keke-NAPEP da ake haya da su musamman da daddare su guji yin haka, domin duk wanda aka kama zai kuka da kansa.Yakubu Soja ya ce jami’ansa ba za su bari a yi amfani da kekuna wajen […]
Shugaban Hadin Gwiwar Jami’an Tsaro na Jihar Kaduna (Operation Yaki) Yakubu Yusuf Soja ya gargadi masu saka labule a Keke-NAPEP da ake haya da su musamman da daddare su guji yin haka, domin duk wanda aka kama zai kuka da kansa.
Yakubu Soja ya ce jami’ansa ba za su bari a yi amfani da kekuna wajen aikata laifuffuka ba.
Yakubu Soja wanda ya sanar da haka ga manema labarai a Kaduna, ya ce daga yanzu za a rika hukunta duk wanda aka kama yana yawo da Keke NAPEP mai labule da daddare.
Shugaban na Operation Yaki wanda kuma har wa yau shi ne Mai bai wa Gwamnan Jihar Shawara kan Harkar Tsaro ya bayyana nasarorin da rundunarsa ta samu wajen yaki da barayin shanu da masu aikata sauran miyagun ayyuka a jihar.
Ya ce “A watannin baya rundunar ta kai samame a dajin Kurmuku da Kuyambana inda muka yi nasarar gano shanun sata sama da dubu tara kuma tuni muka mika wa masu su. Kafin in zo wannan runduna an mayar da ofishinta wajen hira, kuma da muka zo babu motoci masu aiki, muka rubuta wa Gwamna ya amince mu sayo motoci 700 an kuma kaddamar da su yanzu suna aiki. Kuma motocin sun taimaka mana wajen shiga dazuzzuka domin gudanar da ayyukanmu.”
Ya ce sun kuma sun samu nasarar rage ayyukan daba a unguwannin Rigasa da Unguwar Rimi da Hayin Banki da Unguwar Sanusi da Tudun Wada da Cikaji a Zariya da Tuge da Magume da Unguwar kaya da sauransu.
Sai rage aikata miyagun ayyuka a kan tititunan Kaduna zuwa Abuja da Kaduna zuwa Birnin Gwari da Zariya zuwa Kaduna da Saminaka zuwa Jos.