An haramta auren ’yan kasa da shekara 18 a Saudiyya

Ma’aikatar Harkokin Shari’a ta kasar Saudiyya ta haramta aure tsakanin ’yan kasa da shekara 18 sannan ta saka shekara 18 din a matsayin mafi karancin shekarun aure a kasar. Gidan rediyon BBC ya ce Ministan Shari’a, Sheikh Walid Al-Sama’ani ne ya bayar da umarnin ga kotuna, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito a farkon […]

An haramta auren ’yan kasa da shekara 18 a Saudiyya

Ma’aikatar Harkokin Shari’a ta kasar Saudiyya ta haramta aure tsakanin ’yan kasa da shekara 18 sannan ta saka shekara 18 din a matsayin mafi karancin shekarun aure a kasar.

Gidan rediyon BBC ya ce Ministan Shari’a, Sheikh Walid Al-Sama’ani ne ya bayar da umarnin ga kotuna, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito a farkon makon nan.

Batutuwa irin wadannan za a mika su ne ga kotu ta musamman domin duba su a karkashin dokar kare hakkin yara.

Umarnin da Ministan ya bayar yana karkashin lamba ta 16/3 ta dokar kare hakkin yara wadda ya ce: “Kafin a kulla yarjejeniyar aure wajibi mutum ya tabbatar cewa auren ’yan kasa da shekara 18 ba zai zama matsala a gare su ba, sannan da izininsu aka daura shi, mace ko namiji.”

Kasar Saudiyya tana gudanar da sauye-sauye a yunkurinta na sajewa da sauran manyan kasashen duniya da kuma guje wa suka da take sha game da zargin take hakkin dan Adam.

Binciken da BBC ya gudanar ya gano cewa sauye-sauyen da take gudanarwa da kuma tsauraran dokokin kasar na yin kankankan a yanzu.