An haramta fina-finai na faɗan daba da harkar daudu a Kano

Mun ba wa masu shirya wannan fina-finai wata ɗaya su gyara ayyukansu kafin doka ta fara aiki a kansu.

An haramta fina-finai na faɗan daba da harkar daudu a Kano

Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha. (Hoto: Twitter/@abbaelmustaph1)

Gwamnatin Kano ta haramta yin duk wasu fina-finai da ke nuna faɗan daba ko harkar daudu nan take a faɗin jihar.

Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Kano ce ta ɗauki wannan mataki biyo bayan korafe-korafen da al’umma ke yi a kan shirya fina-finan da ke nuna faɗan daba da harkar daudu a jihar.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a Yammacin wannan Larabar.

Sanarwar ta ambato Shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha ya ba da umarnin dakatarwa tare da hana dukkan fina-finan da ke nuna faɗan daba da harkar daudu a faɗin jihar jim kaɗan bayan wata ganawa da ya yi da manyan ma’aikatan hukumar.

Aminiya ta ruwaito cewa, ganawar Shugaban hukumar tace fina-finan ta haɗa da wasu daga cikin wakilan ’ya’yan masana’antar shirya fina-finan ta kannywood ciki har da kungiyoyin MOPPAN, Arewa Film Makers, Darektoci da Furodusoshi.

Abba El-Mustapha ya ce “doka ce ta ba wa hukumar damar dakatarwa ko hana duk wani fim da take ganin ya ci karo da tarbiya da al’adar al’ummar Kano.

“Saboda haka tuni lokaci ya shige da za a saka ido irin wannan gurbatattun fina-finai su ci gaba da yaduwa a cikin al’umma.

Abba El-Mustapha ya kuma gode wa ’yan masana’antar Kannywood dangane da haɗin kai da kuma goyan bayan da suke ba wa hukumar a koda yaushe.

“Ina kuma gode wa al’ummar Jihar Kano kan irin haɗin kan da suke ba wa Hukumar musamman wajen sanar da ita duk wani abu da suke ganin ya saba da al’ada da tarbiyar addinin musulunci.

Abba El-Mustapha ya kuma yi alkawarin ci gaba da barin kofarsa a buɗe domin karɓar shawarwari ga duk wanda suke da buƙatar hakan.

A ƙarshe ya ba wa masu shirya irin wannan fina-finai na faɗan daba ko harkar daudu damar wata ɗaya da su gyara ayyukansu kafin dokar ta fara aiki gadan-gadan a kansu.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos