An haramta hawa babur a Jalingo

Gwamna Agbu Kefas na Jihar Taraba ya haramta hawa babur a birnin Jalingo nan take.

An haramta hawa babur a Jalingo

Babura

Gwamna Agbu Kefas na Jihar Taraba ya haramta hawa babur a birnin Jalingo nan take.

Gwamnan ya sanar da dokar ce jim kadan dan zaman kwamitin tsaron jihar a yammacin Litinin din nan.

Zaman wanda Gwamna Kefas ya samu wakilin mataimakinsa, Aminu Abdullahi Alkali, ya samu halarcin shugabannin hukummin tsaron jihar.

Mataimakin gwamnan ya ce taron ya yi bitar ayyukan masu babura da ma babura masu kafa uku a jihar, inda daga karshe aka ka takaita amfani da babura masu kafa uku zuwa daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe.

Haka zalika an kafa kotunan tafi da gidanka domin hukuntawa da kwace baburin duk wanda aka samu da karya dokar.

Aminiya ta gano cewa an kasa dokar ce saboda karuwar matsalar tsaro a jihar.

An dawo da wutar lantarki a Kaduna

An kashe ɗan banga da yin garkuwa da ’yan mata 6 a Neja

’Yan fashin teku sun sace jirgin fasinja mutum 11 sun ɓace a Ribas

Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace