An haramta luwadi a Uganda
Shugaban kasar Uganda Mista Yoweri Musebeni ya sanya hannu a kan wata sabuwar doka wadda ta haramta luwadi a kasar, wadda kuma ta jawo ka-ce-na-ce a tsakanin kasar da kasashen Yammacin Duniya.Dokar ta tanadi hukuncin zaman gidan kurkuku na lokaci mai tsawo ga wadanda suka aikata luwadi.Shugaban ya sanya hannu ne a gaban jami’an gwamnatin […]
Shugaban kasar Uganda Mista Yoweri Musebeni ya sanya hannu a kan wata sabuwar doka wadda ta haramta luwadi a kasar, wadda kuma ta jawo ka-ce-na-ce a tsakanin kasar da kasashen Yammacin Duniya.
Dokar ta tanadi hukuncin zaman gidan kurkuku na lokaci mai tsawo ga wadanda suka aikata luwadi.
Shugaban ya sanya hannu ne a gaban jami’an gwamnatin kasar da kuma manema labarai.
Shugaba Musebeni ya jingine sanya hannu kan daftarin kudurin dokar domin ya ba masana kimiyya damar gudanar da bincike a kan ko ana haihuwar mutum dan luwadi ne ko kuwa sa kansa yake yi.
Tun farko daftarin kudurin dokar da aka gabatar a shekarar 2009, ya tanadi hukuncin kisa ne a kan duk luwadi ko ’yar madigo, amma daga baya aka yi masa gyaran fuska, aka soke hukuncin kisa aka sanya dauri a gidan yari ga wanda aka samu da laifin neman jinsi daya.
Shugaba Musebeni ya ce, masana kimiyya na Uganda ne za su gudanar da binciken, kuma masu aiko da rahotanni, sun ce Shugaban yana tauna taura biyu ne – wato yana nema ne ya faranta ran masu zabe a kasar da ke goyon bayan dokar a gefe daya ya faranta wa Turawan Yamma masu ba da agaji.
Tuni Jakadan Amurka a Kampala, Scott Delisi ya shaida wa BBC cewa yana bukatar karin haske game da dokar hana luwadin kafin Amurka ta yanke hukuncin ko za ta ci gaba da tallafa wa kasar musamman a kan yaki cutar kanjamau ko a’a.
Mista Delisi ya ce yana bukatar tabbaci cewa ma’aikatan Amurka da kawayenta ba za su fuskanci daurin gidan yari a kasar kan dokar ba.
Jakadan ya kuma soki wata jaridar Uganda saboda wallafa jerin sunayen wadanda ta kira manyan ’yan luwadin kasar.
Shugaba Obama na Amurka ya yi gargadin cewa dangantakar Amurka da Uganda za ta lalace idan gwamnatin Ugandan ta sanya hannu kan dokar hana yin luwadin.