An haramta masu tallar maganin gargajiya da kalmomin batsa a Katsina
An haramta tallar maganin gargajiya da kalmomin batsa a duk faɗin masarautar ta Katsina. Kazalika, an hana yin tallace-tallace ta irin yadda ake buɗe na’urar amsa kuwa da ƙarfi a masallatai da wuraren taron jama’a saboda tana damun jama’a a lokacin da suke gudanar da harkokin su na yau da kullum. Shugaban kungiyar masu sayar […]
An haramta tallar maganin gargajiya da kalmomin batsa a duk faɗin masarautar ta Katsina.
Kazalika, an hana yin tallace-tallace ta irin yadda ake buɗe na’urar amsa kuwa da ƙarfi a masallatai da wuraren taron jama’a saboda tana damun jama’a a lokacin da suke gudanar da harkokin su na yau da kullum.
Shugaban kungiyar masu sayar da maganin gargajiyar Malam Ilyasu Salisu wanda aka fi sani da suna Malam Zakiru ya shaida wa Aminiya haka a yayin da suke hira da shi a kan ayyukan ƙungiyar. Ya ƙara da cewar masarautar har ila yau ta umarci kungiyar da ta ci gaba da tantance masu sayar da magungunan garjiya domin fitar da gurbatattu da kuma mayaudara, aikin da shugaban ya ce tuni suka fara aiwatar da shi a dukkan ƙananan hukumomi 34 da ke cikin jihar.
“Ƙungiya na da tsare-tsare da kuma takardun cikewa na shaidar ta amince da magani ko mai tallar maganin bayan kuma kullum tana ƙoƙarin ganin cewa tana aiki kafada da kafada da hukumar NAFDAC domin tantance magani da kuma bayar da takardar shaidar amincewa da wannan magani. Har ila yau, ƙungiya na duba tsaftar magani da inda aka zuba shi domin tabbatar da cewa bai gurbace ba”. Malam Zakiru ya ce ƙungiyarsu na sa ido sosai a kan baƙin masu tallar maganin gargajiyar da suka mayar da Katsina tamkar wata kasuwar magani.
“Duk wani baƙon mai sayar da magani in ya shigo sai mun san daga inda ya fito, takardunsa na shaida da sauransu, wasu lokutan ma har muna bi ta ƙarƙashin ƙasa don tabbatar da gaskiyar abin da ya faɗi. Batun ‘ya’yan ƙungiya da ayyukan kuwa,sai dai mu yi godiya ga Allah, domin bakin gwargwado muna ƙara samun haɗin kai tsakaninmu ba kamar baya ba. Kullum ƙara samun sabbin membobi muke yi. Kuma muna samun goyon bayan masarauta da sauran jami’an tsaro da ke cikin jihar baki ɗaya”.
Ya ƙara jan hankalin ‘ya’yan ƙungiyar da su kiyaye yin ha’inci ko bayar da maganin ƙarya ga mai lalura don kawai su samu kuɗi. “Idan har ka san ba ka da maganin lalurar da aka kawo maka, to ka nemi wanda ka san yana da maganin domin shi ma wata rana zai kawo maka irin naka. Amma yaudara ga batun harkar lafiya ba ƙaramar cuta ba ce wadda kai ba ka iya maganinta. Don haka mu riƙe gaskiya a wajen sana’arrmu sai Allah ya taimake mu” in ji shi.