An haramta rawar solo a Jihar Kano

Hukumar Tace Fina-finai da dab’i ta Jihar Kano ta bayar da sanarwar hana rawar solo a fadin jihar.Shugaban hukumar, Malam Isma’ila Na’abba Afakallah ya bayyana wa Aminiya cewa hukumarsa ta damu matuka game da yadda masu gidajen rawa da aka fi sani da gidajen gala ke shirya wa ’yan mata biki suna hawa kan dabe […]

An haramta rawar solo a Jihar Kano
An haramta rawar solo a Jihar Kano

Hukumar Tace Fina-finai da dab’i ta Jihar Kano ta bayar da sanarwar hana rawar solo a fadin jihar.
Shugaban hukumar, Malam Isma’ila Na’abba Afakallah ya bayyana wa Aminiya cewa hukumarsa ta damu matuka game da yadda masu gidajen rawa da aka fi sani da gidajen gala ke shirya wa ’yan mata biki suna hawa kan dabe suna rawa da niyyar neman kudi, inda ya ce hakan abu ne da kai tsaye ke lalata tarbiyyar yaran jihar.
A cewasa: “Yawacin ’yan mata da ke gudanar da wannan abu, su ne ire-iren da ke zuwa Kano da niyyar shiga fim din Hausa amma su buge da yin rawar solo, inda masu irin wadancan gidajen rawar suke daukar su suna shirya musu irin wannan raye-rayen wanda suke gudanarwa a dabe kowa na kallonsu. A wanann rawar za ka ga ’yan matan sun sanya wando da ’yan kananan riguna suna ta tikar rawa a gaban mutane. Kai ko hijabi masu rawar nan za su rika sanyawa ba za mu yarda da hakan ba, domin abu ne da bai dace ba. Don haka ba za mu zuba ido hakan ya ci gaba da faruwa ba, musamman idan aka yi la’akari da barnar da hakan ka iya haifarwa a tsakanin al’ummarmu. Yara da matasa mutane ne masu kwaikwayo da saurin daukar abubuwa a kansu, don haka wanann dabi’a na iya yin tasiri a rayuwarsu, wanda ba za mu so hakan ba.”
Ya ce dokar ba ta shafi masu rawar koroso ko masu shirya wasan kwaikwayo na dabe ba. Da yake bayanin hukuncin da hukumar ta tanadar a kan masu rawar, ce hukumarsu na da kotun tafi da gidanka don
haka za su gurfanar da duk wanda ya yi kunnen uwar shegu da wannan umarni.