An haramta shan barasa saboda tsananin zafin rana a Paris
Sabuwar dokar ta tanadi haramta shan barasa daga ƙarfe 12 na rana zuwa ƙarfe 7 na safe a ranakun Juma’a da Asabar.
Mahukunta a birnin Paris na ƙasar Faransa sun sanar da haramta saye da shan barasa a wuraren da jama’a ke taruwa, sakamakon matsin lambar da asibitoci ke fuskanta yayin da ƙasar ke fama da tsananin zafin rana.
Shugaban ’yan sandan Paris, Patrice Faure, ya ce asibitoci a birnin da kewaye sun kusa cika maƙil saboda ƙaruwar masu neman kulawar lafiya sakamakon zafin rana.
- Venezuela na ci gaba da samun tallafi bayan mummunar girgizar ƙasa
- ’Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban APC a Kebbi
“Mun kai wani matsayi da cibiyoyin lafiya ke fama da cunkoso, kuma adadin mutanen da ake kwantarwa na ci gaba da ƙaruwa,” in ji Faure yayin ganawa da manema labarai.
Sabuwar dokar ta tanadi haramta shan barasa a tituna da sauran wuraren taron jama’a daga ƙarfe 12 na rana zuwa ƙarfe 7 na safe a ranakun Juma’a da Asabar.
Haka kuma, an haramta sayar da barasa ta hanyar ɗauka daga shaguna daga ƙarfe 6 na yamma zuwa ƙarfe 7 na safe a waɗannan kwanaki.
Sai dai dokar ba ta shafi gidajen cin abinci da mashaya da ke da izinin gudanar da harkokinsu a wuraren da aka ware musu ba.
Faure ya ƙara da cewa rundunar kashe gobara ta Paris ta samu ƙaruwar ayyuka sosai, inda yawan kiran gaggawa da ta amsa ya haura 2,500 a ranar Alhamis kaɗai.
Mahukunta sun bayyana cewa matakan na daga cikin ƙoƙarin rage matsin lamba kan asibitoci da kuma kare lafiyar jama’a yayin wannan matsananciyar guguwar zafin rana da ta mamaye sassan Faransa.