An haramta wa dalibai Musulmi yin azumi a wasu makarantun Ingila

Makarantun firamare da dama a Landan sun hana dalibansu yin azumi Ramadan na bana daa aka fara a jiya, da sunan nuna damuwa kan lafiyar yaran. Makarantar Barclay School da wasu uku da suka hada da Lion Academy Trust Schools, sun aika wa iyaye wata wasika a ranar 10 ga Yuni cewa, azumin Ramadan na […]

An haramta wa dalibai Musulmi yin azumi a wasu makarantun Ingila
An haramta wa dalibai Musulmi yin azumi a wasu makarantun Ingila

Makarantun firamare da dama a Landan sun hana dalibansu yin azumi Ramadan na bana daa aka fara a jiya, da sunan nuna damuwa kan lafiyar yaran.

Makarantar Barclay School da wasu uku da suka hada da Lion Academy Trust Schools, sun aika wa iyaye wata wasika a ranar 10 ga Yuni cewa, azumin Ramadan na bana ya zo a lokacin tsananin zafi kuma a lokacin da ake gudanar da wasanni da sauran ayyukan karshen shekarar karatu.
Takardar makarantar dauke da sanya hannun “Mista Wright, Mukaddashin Shugaban Makaranta,” an kuma tura ta a shafin intanet na makarantar, inda ta ce jami’an makarantar “sun tambayi malamai” kuma an shaida musu cewa dokokin Musulunci bas u bukaci yara su yi azumi ba.
Takardar ta ce duk mahaifin da ke so da ko ’yarsa su yi azumi a ranar makaranta, sai ya gana da shugaban kowace makaranta don tattauna yadda za a tabbatar da lafiya da jin dadin yaron. “Kuma ba za a bar yaro ya zo makaranta yana azumi ba, sai mahaifi ya gana da shugaban makaranta,” inji sanarwar.
kungiyar Musulmin Birtaniya na cikinkungiyoyin Musulmin da suka soki wannan mataki, inda suka ce Musulunci ya tsara ka’idoji da hanyoyin kare yaran a lokacin Ramadan ba sai ya samu taimakon daga wajensa ba, kamar yadda jaridar Daily Edpress ta ruwaito.
A ranar Juma’ar da ta gabata, kwana biyu bayan an tura wa iyaye takardar, an sanya sanarwar a shafin makarantar Lion Academy Trust na intanet dauke da sanya hannun Babban Daraktan Makarantar Justin James.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos