An haramta wa manyan tireloli aiki a Najeriya

Gwmanatin Tarayya ta haramta wa tireloli masu ɗaukar man fetur lita 60,000 aiki a Najeriya

An haramta wa manyan tireloli aiki a Najeriya

Gwmanatin Tarayya ta haramta wa tireloli masu ɗaukar man fetur da nauyinsa ya kai lita 60,000 aiki a Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris mai kamawa.

Hukumar Albarkatun Man Fetur ta Kasa (NMDPRA) ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne da nufin taƙaita yawan haɗuran tirelolin man fetur da ke sanadiyyar asarar ɗaruruwan rayuka da dukiyoyi na miliyoyin kuɗaɗe.

Hukumar ta ƙara da cewa zuwa ƙarshen wannan shekara ta 2025 za a haramta wa motoci masu ɗaukar man fetur lita 45,000 hawa titunan Najeriya.

Ta bayyana cewa bayan wani taron da aka gudanar kan yawan haɗuran tirelolin man fetur da irin asarar da hakan ke haifarwa, masu ruwa da tsaki a harkokin mai da sufuri hukumomin tsaro da sauransu sun yi ittifakin cewa a haramta wa tireloli masu ɗaukar man fetur da ya kai lita 60,000 hawa titi da kuma daukar mai a tashoshin sayar da man a faɗin Najeriya.

 

Ogbugo Ukoha, wanda shi ne Babban Daraktan Jigila na NMDPRA ya kara da cewar taron ya alaƙanta hatsarin motocin da nauyin kayan da motocin suke dauka kuma suka amince da ɗaukar matakin.

Ya bayyana cewa ƙaruwar hatsarin motocin musamman yadda ake samun asarar rayuka a lokacin da mutane ke zuwa kwasar man da ke tsiyaya.

Ukoha ya ce ganin yadda munin hatsarin ke ƙaruwa ya sa ɗaukar matakin ya zama dole.

Kungiyar NATO ta masu ababen haw ta koka da cewa matakin da gwamnati ta ɗauka zai jawo wa mambobinta asarar kimanin Naira biliyan 300.

Shugaban Ƙungiyar NATO, Yusuf Uthman, alaƙanta aukuwar haɗuran da rashin kyan hanyoyi da yanayin lafiyar motocin da kuma direbobi.

Ya ce mambobin kungiyar suna da tirela mai daukar lita 60,000 akalla guda 2,000 wadda kowacce kuɗinta ta kai Naira miliyan 150.

Don haka muddin aka hana motocin yin aiki to asarar da za su yi ta kai ta Naira biliyan 300.

Daga nan sai ya roki gwamnati ta shiga cikin lamarin ta hanyar saye motocin daga hannunsu domin rage musu raɗaɗi.

An haifi alade mai fuskar mutum a Philippines

Ko Real Madrid za ta iya lashe Gasar Zakarun Turai bana?

Haɗarin mota ya laƙume rayuka 12 a Neja

Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kano ta raba kayan tallafi