An haramta wa Sarakunan Zamfara ba da izinin haƙar ma’adanai

Dokar wadda ta fara aiki nan take an sanya mata hannu a wannan Alhamis din a Gusau.

An haramta wa Sarakunan Zamfara ba da izinin haƙar ma’adanai

Gwamna Dauda Lawal Dare ya rattaba hannu a kan dokar haramta wa sarakunan gargajiya ba da izinin hakar ma’adinai a fadin Jihar Zamfara.

Dokar wadda ta fara aiki nan take an sanya mata hannu a wannan Alhamis din a Fadar Gwamnatin Zamfara da ke Gusau.

Cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnatin jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa dokar da gwamnan ya sanyawa hannu za ta dakile ababen da ke kara rura wutar ta’addancin ’yan bindiga a jihar.

Mai magana da yawun gwamnan ya ce wannan doka ta dakatar da duk wata takardar ba da izinin hakar ma’adinai “wadda ta hada da daidaikun mutane ko kamfani ko kungiyoyi dake aiyukkan hakar ma’adinai.”

A jawabin da gwamnan ya yi yayin rattaba hannu kan sabuwar dokar, ya bayyana cewa an dauki matakin ne domin samar da mafitar da za ta dakile ayyukan ’yan daban daji da masu garkuwa da mutane.

“A yau gwamnati ta bullo da daya daga cikin hanyoyin kawo karshen matsalar tsaro. Saboda haka ne na sanya dokar haramta wa sarakuna a dukkan kananan hukumomin Zamfara 14 bayar da izinin hakar ma’adinai.

“Babban Alkalin jihar nan ya ce harkar tono ma’adinai tana cikin abubuwa na gaba-gaba da ke ba da gudunmuwa wurin kara tabarbarewar tsaro a jihar musamman ta’adar ’yan daban daji,” a cewar Dauda.

Ya kara da cewa, “duk wata gwamnati da ta san abin da ya kamata dole ne ta dauki matakin hana hakar ma’adinai da ake yi ba bisa ka’ida ba wanda shi ne yake haifar mana da rikici a jihar nan.”

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai