An haramta wa Sojaboy harkar Kannywood
Hukumar tace finafinai ta kwace lasisin mawaƙi Sojaboy da jaruma Shamsiyya Muhammad da jaruma Hassana Suzan tana mai umartar masu gidajen wasa da masu harkar Kannywood su guji yin aiki da su domin guje wa fushin doka
Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta haramta wa mawaƙi Usman Sojaboy da wasu jarumai mata biyu shiga harkokin fim ko waƙa da dangoginsu a jihar.
Hukumar ta kwace lasisin Sojaboy da jaruma Shamsiyya Muhammad da jaruma Hassana Suzan tana mai umartar masu gidajen wasa da sauran masu harkar fim da dangoginsu da su bi umarnin sau da ƙafa.
Shugaban Hukumar Abba El-mustapha ya bai wa sashin tace fina-finai na Hukumar umarnin kada ya ƙara tace duk wani fim ko waƙa da Sojaboy ko matan suka fito a ciki.
Sanarwar da kakakin Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar ta ruwaito Abba Al-Mustapha yana kira ga masu shirya fina-finai musamman daraktoci da su kiyayi yin duk wata huldar aiki da su Sojaboy domin guje wa fushin Hukumar.
- NAHCON ta sanar da kuɗin kujerar Hajjin 2025
- Yadda aka yi jana’izar mutane 86 bayan fashewar tankar mai a Dikko Junction
- Za a biya ’yan Najeriya miliyan 70 tallafin N75,000 don rage talauci
Abdullahi Sani Suleiman ya ce Hukumar ta dakatar da su Sojaboy ne saboda ƙorafe-ƙorafen al’umma da malaman Musulunci a Jihar Kano kan salon wakar da mawaƙin yake ƙoƙarin fitowa da shi a wanda ya saɓa da koyarwar Musulunci da al’adar malam Bahaushe.
A cewarsa, Hukumar na yin iya kokarinta wajen gargaɗar masu irin wannan halayya da su guji yin duk wani abu da zai zubar da kimarsu ko ta sana’arsu, domin hukumar ba za ta lamunci duk wani abu da zai taɓa addini, al’ada ko tarbiyyar a’lummar Kano ba da sunan sana’a.
A watan da ya gabata ne dai Hukumar ta dakatar da jarumar Kannywood, Samha M Inuwa, saboda shigar banza, da nufin tsaftace masana’antar.
A baya-bayan nan Sojaboy ya yi ƙaurin suna bisa irin wasu bidiyon da yake runguma da ɗaukar mata a soshiyal midiya, wanda ya jawo masa caccaka daga abokan sana’arsa da ma ’yan kallo.