An haramta wa yara aikin karfi bayan mutuwar takwas a Kaduna
An dakatar da yin amfani da kananan yara daga yin aikin karfi musamman a gonaki a Karamar Hukumar Kubau ta Jihar Kaduna. Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Sabo Aminu Anchau, ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Kaduna. Alhaji Sabo ya fayyace yadda wasu almajarai takwas suka mutu a hatsarin […]
An dakatar da yin amfani da kananan yara daga yin aikin karfi musamman a gonaki a Karamar Hukumar Kubau ta Jihar Kaduna.
Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Sabo Aminu Anchau, ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Kaduna.
Alhaji Sabo ya fayyace yadda wasu almajarai takwas suka mutu a hatsarin jirgin ruwa a kan hanyarsu ta dawowa daga yi wa malamansu aikatau a gonaki.
- Sojoji sun halaka ’yan bindiga a Kudancin Kaduna
- Ganduje zai biya kudin karatun daliban Kwankwasiyya miliyan N258
Yayin da yake bayyana bacin ransa, Alhaji Sabo ya ce galibin malaman makarantun allo na tara almajirai ne kawai da zummar su rika yi masu kwadago a gonakinsu.
Ya ci gaba da cewa ba wai suna kyamatar karatun allo ba ne, sai dai suna kokarin ganin an tsaftace tsarin almajiranci tare da inganta shi ta yadda zai amfani manyan gobe.