An harbe ɗan takarar ciyaman na APC a Ogun

Ganau sun shaida cewar maharan sun harbi ɗan takarar a kai da harsashi.

An harbe ɗan takarar ciyaman na APC a Ogun

Wasu mahara sun harbe ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen kananan hukumomi mai zuwa na Jihar Ogun, Adeleke Adeyinka har lahira.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Asabar a yankin Jide Jones da ke Abeokuta.

Ganau sun bayyana cewar wasu ’yan bindiga ne a cikin mota mai duhu suka fasa masa kai da alburushi.

Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da kisan, inda ta bayyana cewar maharan sun yi amfani da bindiga ne wajen kisan sannan suka tsere bayan sun kashe shi.

Hukumomi na ci gaba da ƙoƙarin gano wadanda suka aikata laifin.

Ƙungiyar matasan jam’iyyar APC, ta yi Allah-wadai da kisan, tare da yin kira da a gudanar da cikakken bincike don ganin an yi adalci.

Al’umma yankin na cikin ɗimuwa bayan kisan ɗan takarar kujerar shugaban ƙaramar hukuma a jihar.

’Yan kasuwa da dama a yankin sun rufe shagunansu saboda tsoron aukuwar wani tashin hankalin.

Mazauna yankin sun yi kira da a tsaurara matakan tsaro don kauce wa sake aukuwar irin wannan tashin hankali.

Ƙungiyar matasan, ta bayyana Adeleke a matsayin matashi mai cike da burin ci gaban al’umma da kuma yi wa jam’iyyarsa hidima.

Sun buƙaci ’yan sanda su ƙara ƙaimi wajen kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da ɗaukar matakan tsaro don hana aukuwar irin wannan a gaba.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC