An harbe dan majalisar wakilai a jihar Oyo

Dan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazabar Lagelu da Akinyele a Ibadan Hon. Temitoye Olatoye Sugar ya gamu da ajalinsa da yammacin yau misalin karfe 4 zuwa 5 a inda wasu mutane da ba a san ko suwane ne ba suka harbe shi da bindiga. Wata majiya mai rushe ta tabbatar da mutuwar wannan […]

An harbe dan majalisar wakilai a jihar Oyo

Dan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazabar Lagelu da Akinyele a Ibadan Hon. Temitoye Olatoye Sugar ya gamu da ajalinsa da yammacin yau misalin karfe 4 zuwa 5 a inda wasu mutane da ba a san ko suwane ne ba suka harbe shi da bindiga.

Wata majiya mai rushe ta tabbatar da mutuwar wannan Dan Majalisa wanda ya tsaya takarar kujerar Majalisar wakilai a karkashin inuwar Jam’iyar ADP a zaben da ya gabata a inda yasha kaye daga Jam’iyar APC mai mulki a Jihar Oyo. Majiyar ta ce Hon. Temitoye Olatoye Sugar ya mutu ne a Asibitin koyarwa na UCH a daidai lokacin da aka garzaya da shi asibitin don yi masa jinya.