An harbe ma’aikatan Polio hudu a Pakistan
A shekaranjiya Laraba ne aka harbe wasu ma’aikatan Polio hudu a kasar Pakistan, yayin da wasu uku suka jikkata a birnin kuetta da ke kudu-maso-yammacin kasar a cewar hukumonin.A cewar rundunar ’yan sandar kasar wasu ne da ba a san ko su wane ne ba a kan babura, suka harbe ma’aikatan mata uku da kuma […]
A shekaranjiya Laraba ne aka harbe wasu ma’aikatan Polio hudu a kasar Pakistan, yayin da wasu uku suka jikkata a birnin kuetta da ke kudu-maso-yammacin kasar a cewar hukumonin.
A cewar rundunar ’yan sandar kasar wasu ne da ba a san ko su wane ne ba a kan babura, suka harbe ma’aikatan mata uku da kuma direbansu namiji, inda mata biyu suka mutu nan take, sauran biyu kuma suka cika daga bisani saboda munanan raunukan da suka ji. Kuma a halin yanzu hukumomi sun bayyana dakatar da aikin rigakafin cutar Polio a yankin. A farkon wannan watan ne aka kaddamar da shirin yaki da cutar polio a Birnin kuetta, yankin da ke fama da rikici a kasar.
kasar Pakistan na daya daga cikin kasashen da suka rage masu fama da cutar, sauran su ne Najeriya da Afghanistan. An dai fi dora alhakin kai irin wadannan hare-haren kan masu kishin Islama da ke kallon ma’aikatan a matsayin masu leken asiri ko kuma zargin ruwan maganin na hana haihuwa.
Wadda ke jagorantar hukumar yaki da cutar a kasar, Ayesha Raza Farook ta bayyana wa BBC harin “dabbanci ne”. Ta ce farmakin ya faru ne a daidai lokacin da masu aikin rigakafin suke kokarin karasawa wajen masu samar musu da tsaro.
Fiye da masu aikin rigakafin Polio 60 ne ciki har da masu ba su tsaro da direbobinsu ne aka kashe daga shekarar 2012 zuwa bana. Kuma a bana kadai an samu rahoton cewa wadanda ke dauke da cutar a kasar sun kai mutum 260, alkalumma mafi yawa tun shekarar 2000.