An harbe manomi saboda rikici kan filin kiwo a Borno

Rikici kan filin kiwo tsakanin wani makiyayi da wani manomi ya yi sanadin mutuwar wani manomi mai shekaru 32 a kauyen Muva da ke cikin karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.  

An harbe manomi saboda rikici kan filin kiwo a Borno

Wani manomi a Borno

Rikici kan filin kiwo tsakanin wani makiyayi da wani manomi ya yi sanadin mutuwar wani manomi mai shekaru 32 a kauyen Muva da ke cikin karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.  

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, a ranar 2 ga watan Disamba, 2025, da misalin karfe 4:00 na yamma, Alhaji Usman, wanda ke kiwon shanu, ya samu rashin jituwa da Jauro Ishaya mai shekaru 43, kan rikicin filin kiwo.

A cewar majiyar, yayin takaddamar ne aka zargi Jauro Ishaya da harba bindigar gida wadda ta sami Alhaji Usman a ciki, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

An garzaya da wanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Askira, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa nan take.

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce ta kama wanda ake zargi, kuma tana ci gaba da kokarin kwato bindigar da aka yi amfani da ita a lamarin.

Majiyoyi sun kara da cewa, sashen binciken manyan laifuka (CID) na rundunar ’yan sanda a Maiduguri ya fara gudanar da bincike kan lamarin.