An harbe masu garkuwa da mutane 2 a Abuja

Bayanai sun ce ana zargin ’yan ƙungiyar masu garkuwar na da hannu a sace mutane a yankunan Gwagwalada, Nyanya, Jikwoyi da Karshi.

An harbe masu garkuwa da mutane 2 a Abuja

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya ta kashe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne guda biyu bayan musayar wuta da suka yi da jami’an tsaro a yankin Karshi da ke iyakar Abuja da Jihar Nasarawa.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Abuja, Ahmed Mohammed Sanusi, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 3 ga Mayu bayan jami’an tsaro sun kai samame maɓoyar ‘yan bindigar bayan samun sahihan bayanan sirri.

A cewarsa, an soma musayar wuta ne bayan ’yan bindigar da suka hango jami’an tsaro sun buɗe musu wuta, lamarin da ya yi ajalin shugaban ƙungiyar, Baba Ibrahim wanda ake kira “Tsoho”, da wani Isah Shehu.

Ya ƙara da cewa wasu mutum uku sun tsere da raunukan harbi, yayin da aka kama mutum ɗaya daga cikinsu.

Jami’an tsaron sun kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, da wata ƙaramar bindiga ƙirar gida da harsasai 17 a maɓoyar tasu.

Binciken farko ya nuna cewa ƙungiyar na da hannu a sace mutane a yankunan Gwagwalada, Nyanya, Jikwoyi da Karshi, inda ake zarginsu da sace aƙalla mutum 12.

Kwamishinan ya ce ana kuma zargin ƙungiyar da kashe wasu mutane uku bayan karɓar kuɗin fansa har sama da Naira miliyan 60, tare da yi wa wata mata fyade.

Ya ce ana ci gaba da farautar sauran mambobin ƙungiyar da suka tsere, yayin da za a gurfanar da wanda aka kama bayan kammala bincike.