An harbe mutum takwas kusa da barikin Soja a Taraba

Mahara sun harbe mutune takwas har lahira a kusa da ƙofar shiga barikin sojoji dake Takum a jihar Taraba. Mazauna garin Takum sun shaidawa wakilin Aminiya cewa an yi kisan ne da yammacin Talata. Wani shaida da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce waɗanda aka harbe na kan hanyarsu ne ta dawowa daga coci […]

An harbe mutum takwas kusa da barikin Soja a Taraba

Mahara

Mahara sun harbe mutune takwas har lahira a kusa da ƙofar shiga barikin sojoji dake Takum a jihar Taraba.

Mazauna garin Takum sun shaidawa wakilin Aminiya cewa an yi kisan ne da yammacin Talata.

Wani shaida da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce waɗanda aka harbe na kan hanyarsu ne ta dawowa daga coci a wani ƙauye da ke kusa da barkin sojin.

Rikicin kabilanci ya barke a Taraba

Hausawa sun zargi ’yan kabilar Kutep da kashe musu mutane a kauyen Taraba

Ya ce an harbe su ne daf da ƙofar shiga barikin.

Sai dai, kakakin rundunar ƴan sanda a jihar Taraba, SP Usman Abdullahi da mataimakin daraktan yaɗa labarai na rundunar soji Lt. Oni sun ce ba su samu labarin afkuwar lamarin ba.