An harbe shi har lahira a wurin gwajin maganin bindiga

An harbe wani mutum har lahira a lokacin da ake gwajin maganin bindiga da aka hada masa a Jihar Bauchi.

An harbe shi har lahira a wurin gwajin maganin bindiga

An harbe wani mutum har lahira a lokacin da ake gwajin maganin bindiga da aka hada masa a Jihar Bauchi.

Mutumin mai shekaru 43 da wasu mutum hudu sun je daji Damaiwa ne domin a gwada maganin bindiga da wani mai tsubbu ya ba shi a Karamar Hukumar Zaki a jihar.

Harba bindigar da bokan ya yi ke da wuya ta kama mutumin, wanda mazaunin kauyen Damaiwa da ke gudunumar Burasali ne, ya ce ga garinku nan.

Kakakin ’yan sandan Jihar Bauchi, Ahmed Wakil ya ce bayan samun labarin abin da ya faru ’yan sanda suka je wurin suka dauke gawar suka kai ta asibiti, inda likitoci suka tabbatar rai ya yi halinsa.

Ya tabbatar da cewa an kama mutum biyu daga cikin wadanda aka je gwajin maganin bindigar da su, sauran ukun da suka tsere kuma ana neman su.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe