An harbe ’yan sanda biyu a Yobe
A watan Janairun da ya gabata ne gungun wasu ’yan ta’adda suka harbe DSP Ali Pindar, wani jami’in ɗan sanda da ke ofishin.
![An harbe ’yan sanda biyu a Yobe An harbe ’yan sanda biyu a Yobe](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2024/08/police-1.webp)
Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun harbe wasu jami’an ’yan sanda biyu a ofishinsu da ke Kolere a Ƙaramar Hukumar Fune ta Jihar Yobe.
Aminiya ta ruwaito cewa, a watan Janairun da ya gabata ne gungun wasu ’yan ta’adda suka harbe DSP Ali Pindar, wani jami’in ɗan sanda da ke ofishin.
- Netanyahu ya bai wa Hamas wa’adin sakin Isra’ilawan da take garkuwa da su
- Gwamnatin Kano za ta kafa hukumar kula da masu buƙata ta musamman
Bayanai sun ce tun farko dai marigayi DSP Pindar shi ne ya jagoranci tawagar jami’an da ta cafke wani ƙasurgumin ɗan fashi da makami amma daga bisani aka bayar da belinsa.
Wata majiya ta ce bayan bayar da belin nasa ya jagoranci wata tagawar da ta kai hari zummar ramuwar gayya kuma ya yi nasarar kashe DSP Pindar tare da jikkatar da wani sufeton ’yan sanda.
Haka kuma, wata majiyar ta bayyana cewa sabon harin na ranar Lahadi ya auku ne yayin da wani DSP Jantuku Philibus ya yi yunƙurin kama wani da ake zargi.
Sai dai haƙar jami’in ba ta cimma ruwa ba inda gungun masu ta’adar suka far masa kuma suka samu nasarar kashe shi bayan ya samu munanan raunuka.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa ababen zargin sun yi galaba a kan jami’an ’yan sanda biyu yayin da suka je kama su.
A bayan nan dai an samu aukuwar laifuka a yankin kama daga fashi da makami da garkuwa da mutane da sauransu.