An harbi Dan sanda lokacin garkuwa da surukin Buhari
Hukumar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce, jami’an ‘yan sandan da ke ofishin Kusada sun yi yunkurin dakatar masu garkuwa da surukin Shugaba Buhari Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar bayan wani musayar harbi tsakanin su da ‘yan bindigar, inda anan suka harbi Sufetan dan sanda Muntari Maikudi da ke aiki a ofishin. Kakakin hukumar […]
Hukumar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce, jami’an ‘yan sandan da ke ofishin Kusada sun yi yunkurin dakatar masu garkuwa da surukin Shugaba Buhari Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar bayan wani musayar harbi tsakanin su da ‘yan bindigar, inda anan suka harbi Sufetan dan sanda Muntari Maikudi da ke aiki a ofishin.
Kakakin hukumar ‘yan sandan SP Gambo Isah ne ya sanar da hakan a safiyar yau Alhamis ya ce, jami’in dan sandan da aka harba a yanzu haka yana asibitin tarayya da ke Katsina ana yi masa jinya.