An harbi daya daga ‘yan shi’a masu zanga-zanga a Abuja

A yanzu haka Mabiya Kungiyar ‘yan Uwa Musulmi ta Shi’a (IMN) sun mamaye hanyar shiga zauren majalisar dokokin Najeriya a Abuja, inda suke gudanar da zanga-zanga. Mabiya kungiyar na gangamin tsare shugaban su ne da aka yi Ibrahim Zakzakky. Rahoton na bayyana cewa, sun yi ta lalata motocin jama’a a lokacin zanga-zangar, hakan yasa jami’an […]

An harbi daya daga ‘yan shi’a masu zanga-zanga a Abuja

‘Yan Shi’a

A yanzu haka Mabiya Kungiyar ‘yan Uwa Musulmi ta Shi’a (IMN) sun mamaye hanyar shiga zauren majalisar dokokin Najeriya a Abuja, inda suke gudanar da zanga-zanga.

Mabiya kungiyar na gangamin tsare shugaban su ne da aka yi Ibrahim Zakzakky.

Rahoton na bayyana cewa, sun yi ta lalata motocin jama’a a lokacin zanga-zangar, hakan yasa jami’an ‘yan sanda suka fara harbi a sama don dakatar da su.