An harbi tsohon Shugaban Amurka Donald Trump
An harbi Donald Trump a ɓarin kunnensa na dama.
An harbi tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump yana tsaka da jawabi a wani taron yaƙin neman zaɓe a Jihar Pennsylvania.
Nan da nan dai jami’an leken asirin suka yi wa tsohon shugaban ƙasar rumfa tare da lullube shi a yayin da suka kai masa ɗauki.
Hotunan bidiyo da suka karade dandalin sada zumunta na X sun nuna yadda tsohon shugaban ƙasar ya yi gaggawar sunkuyawa tare da riƙe ɓarin kunnensa na dama inda aka harba yana kwararar da jini.
Sai dai gabanin jami’an tsaro su ɗauke shi daga kan dandamalin da yake jawabi, ya ɗaga hannu da alamar jinjina domin magoya bayansa su tabbatar raunin da ya ji ba abin ɗaga hankali ba ne.
Wannan lamari dai ya faru ne a yayin da zaɓen shugaban Amurka ke ƙaratowa kuma wasu manyan jiga-jigai a jam’iyyar Democrat na ƙara nuna adawa ga takarar Shugaba Joe Biden yayin da shi kuma ke cewa babu gudu babu ja da baya.