An horar da malamai 500 akan tsaro a Borno

Kwamitin Shugaban qasa kan Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI) qarqashin jagorancin mataimakin shugaban kwamitin Alhaji Tijjani Tumsah ya kaddamar da shirin horar da malamai 500 akan matakan kare kansu a shiyyoyi uku na jihar Borno. Ya ce, akwai kalubalen da jama’ar yankunan Arewa maso Gabas ke fuskanta, akwai bukatar ilmantar da matasan jihar. Babbar […]

An horar da malamai 500 akan tsaro a Borno

Kwamitin Shugaban qasa kan Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI) qarqashin jagorancin mataimakin shugaban kwamitin Alhaji Tijjani Tumsah ya kaddamar da shirin horar da malamai 500 akan matakan kare kansu a shiyyoyi uku na jihar Borno.

Ya ce, akwai kalubalen da jama’ar yankunan Arewa maso Gabas ke fuskanta, akwai bukatar ilmantar da matasan jihar.

Babbar matsalar da ke fuskantar yankunan bayan rikicin Boko Haram su ne, akwai fargabar rashin tsaron makarantun yara wanda ya hada da rashin ingantattun malamai sakamakon barazanar tsaro. Horarwar zata taimakawa malaman kan ayyukansu.