An horar da manoman tumatir 100 kan dabarun rage tasirin sauyin yanayi

Manoman sun yaba da horon wanda suka ce ya zo a lokacin da ya dace.

An horar da manoman tumatir 100 kan dabarun rage tasirin sauyin yanayi

Aƙalla manoman tumatir 100 da suka haɗa da masu sarrafa tumatir, ’yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki daga jihohin Arewa maso Yamma ne, suka samu horo kan sabbin dabarun noman tumatir da za su taimaka musu su rage tasirin sauyin yanayi.

An gudanar da horon ne a Cibiyar Bincike da Koyar da Aikin Noma ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya.

Mai shirya taron, Dakta Ololade-Latifat Abdulrahman, ta ce an shirya horon ne saboda sauyin yanayi na ci gaba da jefa noman tumatir cikin matsala.

Ta ce sauyin yanayi, rashin tabbas na ruwan sama, tsananin zafi, ƙwari da cututtuka na rage yawan amfanin gona, sannan suna haddasa asara mai yawa bayan girbi.

Ta bayyana cewa tumatir na daga cikin muhimman amfanin gona a Najeriya saboda yana samar da abinci, ayyukan yi da kuma samar wa manoma kuɗaɗen shiga.

A cewarta, koyar da manoma da sauran masu ruwa da tsaki sabbin dabarun noma da adana tumatir zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin gona da kuma rage asara.

Ta ce horon wani ɓangare ne na wani bincike da ke nazarin yadda sauyin yanayi ke shafar manoman tumatir.

Ta ƙara da cewa sakamakon binciken zai taimaka wa gwamnati wajen tsara manufofin noma, tare da inganta ayyukan jami’an wayar da kan manoma.

Ta kuma bayyana cewa an bai wa mahalarta ingantattun irin tumatir da kwandunan roba domin su yi amfani da abin da suka koya, musamman wajen rage asarar tumatir bayan girbi.

Ta buƙaci mahalarta horln su yi amfani da sabbin dabarun da suka koya tare da koyar da sauran manoma a yankunansu.

Ɗaya daga cikin mahalarta taron, Malam Aliyu Umar, jami’in wayar da kan manoma na Hukumar Bunƙasa Aikin Noma ta Jihar Kaduna (KADA), ya ce horon ya ƙara musu ilimi kan hanyoyin zamani na noma da adana tumatir.

Ya ce sabbin dabarun da aka koyar da su za su taimaka wajen rage asarar tumatir bayan girbi.

Ita ma Malama Asibi Hassan, wadda ke noma da sarrafa tumatir a Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, ta ce horon ya zo a daidai lokacin da ake buƙatarsa.

Ta ce horon ya koya musu yadda za su noma, sarrafa, adana da kuma ƙara wa tumatir daraja.

Asibi, ta ce ƙarancin hanyoyin adanawa da sarrafa tumatir na daga cikin abubuwan da ke haddasa tashin farashinsa a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Ta yi kira ga gwamnati da ƙungiyoyin ci gaba su tallafa wa manoma da injinan sarrafa tumatir masu rahusa, na’urorin busar da amfanin gona da hasken rana, gidajen noma na zamani da sauran fasahohin da za su taimaka wajen samar da tumatir a duk shekara.

Ta yaba wa masu shirya taron saboda haɗa horaswa da kuma raba ingantattun iri da kayan adana tumatir.