An horar da matasa 7000 a Jihar Zamfara

Hukumar kula da ci gaba da ba da tallafi ga kananan masana’antu ta kasa (SMEDAN) da hukumar kula da masana’antu(NEDAP) tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Zamfara, sun bayar da horo ga matasa 7000 a kan koyar da su dabarun sana’o’i da noma da kasuwanci. Shugaban Hukumar SMEDAN na kasa, Alhaji Bature Umar Masari ya […]

An horar da matasa 7000 a Jihar Zamfara
An horar da matasa 7000 a Jihar Zamfara

Hukumar kula da ci gaba da ba da tallafi ga kananan masana’antu ta kasa (SMEDAN) da hukumar kula da masana’antu(NEDAP) tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Zamfara, sun bayar da horo ga matasa 7000 a kan koyar da su dabarun sana’o’i da noma da kasuwanci.

Shugaban Hukumar SMEDAN na kasa, Alhaji Bature Umar Masari ya bayyana haka ta bakin wakilinsa, Friday Okpra, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa wajen bude taron kaddamar da horon a Gusau, Jihar Zamfara.
Shugaban ya kara da cewa gwamnati ta fito da wannan tsari ne don taimakon al’ummar kasar nan, kuma shirin ya shafi matasa wadanda suka kammala makarantun gaba da sakandare, wadanda da za a ba bashi na jari don gudanar da aikin noma da bude kananan bude masana’antu da kuma shiga harkar kasuwanci.