An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe
An buƙaci mahalarta taro su nuna ƙwarewa kan dabarun da aka koyar da su.
Shirin Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL) na Jihar Gombe, tare da haɗin gwiwar JEWEL Environmental Initiative, sun horar da mutum 500 dabarun adana ruwan sama a wani taro da aka gudanar a Jami’ar Jihar Gombe.
A yayin taron am mayar da hankali kan dabarun samar da ruwa mai ɗorewa a cikin shirin gyaran magudanan ruwa na kilomita 21, wanda zai amfani yankuna 19.
- Barau ya buƙaci Ganduje ya ƙwato wa APC ƙarin jihohi
- DAGA LARABA: Dalilan da wasu darikun Kirista ba sa bikin Kirsimeti
Ko’odinetan shirin, Dokta Sani Adamu Jauro, ya bayyana cewa shirin zai rage kwararar ruwa, daƙile ambaliya, da kuma ɓarnar da ruwa ke yi.
An kuma rarraba tankunan ruwa 450 don taimaka wa wajen tattara lita miliyan 1.6 a kowace rana, wanda zai kai lita biliyan 4 a shekara 50.
Malam Ismail Bima Maigombawa, Shugaban JEWEL, ya jaddada muhimmancin amfani da tankunan yadda ya kamata domin rage tsadar ruwan sha da magance matsalolin muhalli.
A jawabinsa, Alhaji Musa Abubakar, Marafan Shamakin Gombe, ya yaba wa shirin tare da kira ga mahalartan su guji zubar da shara a magudanan ruwa.
An kuma gudanar da gabatarwa daga masana kan dabarun tattara ruwan sama da hanyoyin warware matsaloli, inda aka buƙaci mahalartan su yi amfani da kayan yadda ya kamata domin samun ingantaccen muhalli.