An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a
Masarautar Katsina ta ba wa dagattai da masu unguwaninta horo a kan sasanta jama’a a matsayin ginshikin samun dauwamammen zaman lafiya.

An ba wa dagattai da masu unguwanin Masarautar Katsina horo a kan sasanta jama’a a matsayin ginshikin samun dauwamammen zaman lafiya.
An gudanar da taron ilmantarwar na tsawon kwanaki uku ne a kan yadda za a assasa zaman lafiya a tsakanin al’umma ta hanyar sasanci don samun aminci mai dorewa.
Shugaban kamfanin tuntuba na Green Horizon, Farfesa Muhammed Sabiu (SAN) ne ya jagoranci taron wanda shirin Kungiyar Kasashe Rainon Ingila ta shirya.
Tun da farko a jawabinsa na bude taron, Sarkin Katsina, Dokta Abdulmuminu Kabir Sarkin Fulani Hamceta Alhaji Aminu Lawal Bagiwa ya wakilta, ya ja hankalin mahalarta da su tsaya domin sanin abin da za a ilmantar da su kasancewarsu na shugabannin al’umma kuma na farko da ake kawo wa koke.
- Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aiki
- Miji ya yi yunƙurin kashe matarsa kan zargin maita a Kano
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba
A nasa bangaren, Gwamnan Katsina, Umar Dikko Radda wanda Sakataren gwamnatin jahar Barista Abdullahi Garba Faskari ya wakilta ya ce, babu yadda za a samu ci gaban gal’umma sai in tana da zaman lafiya.
Ya ce, kara wa juna ilmi a kan abin da ya shafi zaman lafiya ba karamin abu ba ne, domin an samu wani ilmin da ba’a da shi, saboda haka, “ina kara jan hankalinku da ku tsaya domin amfana da abinda za a koya maku.”
Daya daga cikin mahalarta taron, Mai Unguwa Abubakar ya ce, tabbas “A yanzu na kara samun ilmin yadda zan warware wasu matsaloli idan sun taso a cikin jama’a ta ba sai anje ko’ina ba.”