An jawo hankalin makiyaya game da sabon salon kashe musu dabbobi

Sarkin Fulanin Iggo a garin Igaga na Jihar Oyo, Ardo Ahmadu ya koka da sabon salon da wasu batagari a yankin suka samu na sanya wa dabobbinsu guba, domin su ci su mutu. A cewar sarkin, a kwanakin baya ne wasu mutanen yankin suka sanya guba a a cikin rogo, suka warwatsa a kan hanyar […]

An jawo hankalin makiyaya game da sabon salon kashe musu dabbobi
An jawo hankalin makiyaya game da sabon salon kashe musu dabbobi

Sarkin Fulanin Iggo a garin Igaga na Jihar Oyo, Ardo Ahmadu ya koka da sabon salon da wasu batagari a yankin suka samu na sanya wa dabobbinsu guba, domin su ci su mutu.
A cewar sarkin, a kwanakin baya ne wasu mutanen yankin suka sanya guba a a cikin rogo, suka warwatsa a kan hanyar da shanunsu ke bi suna zuwa kiwo, inda a nan take shanunsa guda 15 suka yi mushe bayan sun ci rogon mai guda. Ya ce ya kai kokensa gidan basaraken Yarabawan yankin, a inda shi kuma ya tara mutanen garin domin sanin wanda ya yi aika-aikar amma kowa ya yi biris, ba tare da an gano wanda ya yi ba.
Daga nan ne ya ce ya sanar wa ’yan sanda kana ya garzaya fadar Sarikin Sasa Alhaji Haruna Mai Yasin, ya sanar da shi halin da ake ciki. “Bayan na dawo daga fadarsa sai na tarar wasu karin shanu guda 8 su ma sun kara mutuwa bayan da suka ci rogon mai guda. Ni a yanzu na san sun riga sun cuce ni, na tabka asara amma abin da muke gudu shi ne nan gaba kadan za mu shiga rani kuma bakin Fulani za su shigo mana kuma mutukar hakan ya faru da shanunsu, aka sanya musu guba suka ci suka mutu, to su ba su san su yi hakuri ba kamar yadda mu muka yi, domin su a tafe suke ba matansu da yaransu a tare da su. Don haka muddin aka kashe musu shanunsu, rigima ce za ta tashi. Ka ga kuma dole masifar ta shafe mu, mu da muke mazauna nan shekaru aru-aru. A saboda haka kirana ga hukuma shi ne, ta yi duk abin da ya dace don maganin fitinar da ka iya tasowa. Na shafe fiye da shekara 27 a garin nan, hakan ba ta taba faruwa ba sai a wannan karon,” inji shi.
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake samun wadansu batagari suna yin garkuwa da dattijan Fulani a yankin domin karbar kudin fansa. Haka kuma ya koka da yadda ’yan sanda ke ba da belin wadanda aka kama da aikata garkuwar, a inda ya ce ba su bukatar a rika sakin duk wanda aka samu da laifin, domin a yanzu sukan mika wa ’yan sanda duk wanda suka kama amma muddin za a ci gaba da sakin masu laifin to za su san matakin da za su dauka a kan batagarin koda kuwa ’yayan waye.
Tun da farko dai Shugaban Majalisar Sarakunan jihohin kurmi, Malam Haruna Mai Yasin ne ya shaida wa Aminiya sabon salon kashe shanun na Fulani makiyaya ta hanyar sanya musu guba, a inda ya yi alwashin kai wa Kwamishinan ’yan sandan Jihar Oyo hoton shanun, domin daukar matakin da ya dace. “Kamata ya yi a rika hukunta masu yin wannan mummunan aikin, domin kada gobe ma su sake.  idan ana hukunta su, ana tilasta su su biya shanun da suka kashe, ai gobe ma ba sa sake ba,” inji shi.