An jefa mu cikin tashin hankali da rufe sansanonin ambaliya —’Yan gudun hijira

Iyalai da ke zaman gudun hijira sun shiga ruɗani bayan matakin da Gwamnatin Borno ta ɗauka na rufe sansanonin bayar da agaji ga mutanen da ambaliyar Maiduguri ta shafa

An jefa mu cikin tashin hankali da rufe sansanonin ambaliya —’Yan gudun hijira

Sansanin ‘Yan Gudun Hijira a Sudan

Matakin da Gwamnatin Borno ta ɗauka na rufe sansanonin bayar da agaji ga mutanen da ambaliyar ta shafa a ƙananan hukumomin Maiduguri da Jere ya jefa wasu iyalai cikin rudani.

Wasu da suka tsira daga ambaliyar da suka samu a matsuguni a cikin sansanonin sun ce matakin da gwamnatin jihar ta dauka zai jefa su cikin mawuyacin hali, saboda gidajensu, babu inda za su iya zama.

Sai dai tun bayan faruwar lamarin, jami’an gwamnati da wasu kungiyoyin agaji da ke kula da sansanonin, ke korafin cewa wasu mutanen da ambaliyar ruwan ba ta shafa ba, sun kutsa cikin sansanonin.

Mutanen da suka fito daga yankin Damboa da ke kusa da su da kuma wasu daga garuruwan Bama, Mafa, Dikwa da dai sauransu, sun yi kaura zuwa sansanonin, duk a kokarinsu na karbar abinci da sauran kayayyakin tallafi da aka tanada domin wadanda ambaliyar ta shafa a baya-bayan nan.

An kafa sansanonin ambaliyar ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ke kokarin ganin ta kammala tsugunar da waɗanda rikicin Boko Haram ya na tsawon shekaru 15 ya raba su da garuruwansu.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya ce sansanonin da aka kafa a makarantu bayan ambaliyar ne za a rufe domin ba da damar ci gaba da karatu a fadin jihar baki daya.

Sai dai wakilinmu da ya zagaya birnin ya ga wasu daga cikin mutanen da suka bar daya daga cikin manyan sansanonin, wato Bakassi, kuma da yawa daga cikinsu sun ce jami’an sansanin sun sallame su.

Wata mace mai suna Zara Isa da ta tsira daga garin Fari ta ce har yanzu ruwan yana kusa da gidajensu kuma ba ta san inda za ta dosa ba.

“Na isa wannan sansanin kwanaki shida da suka wuce tare da ’ya’yana shida. Yau kuma sun nemi kowa ya tafi.

“An ba mu abinci da kudi amma ba mu da inda za mu je.

“Mijina yana zaune ne a shingen babbar hanyar da ke kusa da Langalanga.

“Gidan sauro ya a can ya kwanta. Ba mu da inda za mu je,” in ji ta.

some of the flood victim in maiduguri, borno2
Wasu daga cikin wadanda Ambaliyar Maiduguri ta shafa a Jihar Borno

Habiba Idris, daga Ali Kotoko, ta ce tana da ’ya’ya 10, kuma sun koma sansanin ne bayan an kore su daga makarantar Satomi.

“Na yi kwana biyu a nan amma suna neman mu fice daga sansanin a yau; ina kuma za mu je don Alkah?

“Gwamnati ta ba mu abinci da kuɗi amma ba mu san inda za mu je ba.

“Mun gode wa Gwamna Zulum amma ya kamata a ƙara mana lokaci,” in ji ta.

Wata da ta tsira daga garin Bulabulin, y’ta yi ikirarin cewa ambaliyar ta yi mata tsanani fiye da yadda kowa zai iya tunani, tana mai rokon gwamnati da kada ta saka ta cikin ƙarin wahala da kunci.

“Na rasa ’yar’uwata, Adama da ’ya’yanta shida sakamakon ambaliyar ruwa.

“A karo na karshe da na ganta shi ne na ƙwanƙwasa kofarta na shaida mata cewa ruwan ya mamaye yankin gaba ɗaya.

“Da sauri ta koma domin ta ɗauko ’ya’yanta amma ruwan ya yunƙuro sai na gudu don tsira da raina.

“Zan rayu ina ganin kaina da laifin rashin tsayawa a baya don taimakawa, ”in ji ta.

Rabi Ibrahim, ta ce ruwan dare ya jefa ta a kan titi, tare da ’ya’yanta bakwai.

“Mun leka gidanmu lokacin da ruwa ya ja.

“Ambaliyar ta tafi da rufin gidan da kuma katangar baya. Hasali ma, mutum ba zai iya shiga gidan ba saboda ginin kofar ya ruguje,” inji ta.

Za mu ba su tantuna —Kwamishina

Sai dai kwamishinan yada labarai, Usman Tar, ya ce za a samar da tantuna na wucin gadi domin wadanda suka tsira su kafa a gidajensu.

Ya ce gwamnati za ta tantance irin barnar da ambaliyar ta yi tare da taimaka musu wajen sake gina gidajensu.

Tun bayan barkewar ambaliya, jihar ta samar da sansanonin ’yan gudun hijira 36 domin kula da dubban mutanen da ambaliyar ta shafa.

A lokacin da wakilinmu ya zagaya wuraren da ruwan ya shafa, ya ga yadda gidaje da dukiyoyin gwamnati gami da matsalolin muhalli.

Ɗoyi a Maƙabartar Gwange

Lokacin da wakilinmu ya ziyarci yankin Maƙabartar Gwange, mazauna wurin sun koka a kan ɗoyin da ke fitowa daga maƙabartat.

Makabartar Gwange ita ce mafi girma kuma mafi daɗewa a Maiduguri, inda aka binne dubban mutane.

Da yake zantawa da wakilinmu, ɗaya daga cikin ’yan tsirarun mutanen da ke zaune a yankin ya ce ma’aikatan kula da muhalli da gwamnati ta turo sun wa makabartar feshi.

Ɗaya daga cikinsu mai suna Umara Baana ya ce: “Ruwan nan ya lalata kaburbura da dama, kuma kasar ta yi sako-sako yadda ba za a iya tafiya a kanta cikin sauƙi ba, lamarin da ya hana mutane shiga su gyara ƙaburbura.

“Don haka duk yankin yana wari, ƙazantacce ne, kuma gine-ginen yankin ba za iya zama cikinsu ba.

“Ya kamata gwamnati ta kara ba mu lokaci don gyata gidajenmu da muhallinmu kafin ta rufe sansanonin,” in ji Umara.

Wa’adin makonni biyu

Ana iya tuna cewa a ranar Laraba kwamishina Tar ya ba da sanarwar shirin sansanoni 32 cikin makonni biyu, idan aka fara lissafi daga ranar Litinin.

A cewarsa, ana sa ran cikin lokacin ruwan ambaliyar ya janye ta yadda za a iya komawa da zama a gidajen da abin ya shafa.

Zulum ya yi ƙarin haske

Duk da haka, yayin da yake karbar jami’an Majalisar Dinkin Duniya a gidan gwamnati da ke Maiduguri,, Zulum ya ce wadanda gidajensu ke cike da ruwa ba za su bar sansanonin ba.

Sai dai ya yi gargadin a daina bude wasu cibiyoyin ba da agaji ba gaira ba dalili.

Ya kuma ce za a rufe sansanonin da aka kafa a makarantu domin baiwa yara damar komawa azuzuwansu.

“Abin takaici, mun fahimci cewa galibin mutanen da ke shiga sabbin sansanonin da aka bude ba su ne ainihin wadanda bala’in ambaliya ya rutsa da su ba.

“Bari in gaya muku wani labari. Na je makarantar Sakandaren ’yan mata ta Yerwa inda na jagoranci raba kudade da abinci da sauransu.

“Abin mamaki lokacin da na je filin jirgin Gomari sai na ga mutane dauke da buhunan shinkafa da sauran kayayyaki sun nufi hanyar Gomari inda ba a samu wata ambaliyar ba.

“Hakan ya nuna cewa da yawa daga cikin mutanen da ke cikin sansanonin ba wadanda abin ya shafa ba ne.

“Muna bukatar taimakon Majalisar Dinkin Duniya wajen sake gina gidaje, asibitoci, makarantu da muhimman ababen more rayuwa.

“Muna so mu yi amfani da wannan damar don gode wa Majalisar Dinkin Duniya, duk masu ruwa da tsaki da kuma ɗaiɗaikun mutane da suka taimaka mana a wannan mawuyacin lokaci,” in ji shi.

Da take mayar da martani a madadin tawagar majalisar dinkin duniya, mataimakiyar mai kula da ayyukan jin kai na kasa, Esty Sutyoko, ta bayyana halin da ake ciki na ambaliyar ruwa a Maiduguri a matsayin “rikicin cikin rikici”.

Ta yi kira ga gwamnan da ya taimaka wajen samar da matsuguni kafin mayar da ’yan gudun hijirar zuwa gidajensu.

Kazalika ta yaba wa gwamnan bisa jajircewarsa na ganin ya kawar da wahalhalun da jama’a ke ciki.

Sannan ta yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da ofishin mai baiwa jihar shawara kan harkokin jin kai da ci gaba, Dakta Mairo Mandara domin magance matsalar ambaliyar ruwa cikin gaggawa.